Yan bindiga sun sake kai hari a Bayelsa, wannan karon sun kashe Honarabul Odeinyefa Ogbolosingha, shugaban matasa kuma jigon PDP.
An rahoto cewa yan bindigan sun bindige Ogbolosingha ne har lahira awanni bayan an sallamo matarsa daga asibiti Jihar Bayelsa.
Yan bindiga da ake ce sanye da kayan sojoji sun bindige Hon Odeinyefa Ogbolosingha, shugaban matasa kuma jigon PDP a Jihar Bayelsa.
Ogbolosingha, mai shekaru 53, ma’aikaci ne a gwamnatin jihar Bayelsa a sakateriya da ke Okordia/Zarama Development Board, The Nation ta rahoto. Rahotanni sun nuna cewa an kashe shi ne awanni bayan sallamo matarsa daga asibiti.
Yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji Sun Kashe Fitaccen Jigon Jam’iyyar PDP a Bayelsa. Hoto: Ebiowei Odigiri.
Lamarin, da ya faru a Mechanic Village kan hanyar Edepie-Imiringi road a Yenagoa, babban birnin jihar ta janyo hatsaniya a unguwar.
An gano cewa yunkurin da fusatattun matasa suka yi a unguwar don dakatar da maharan bai yi nasara ba.
Mutuwar Ogbolosingha: Mutane sun nuna damuwa Mutanen gari da suka yi magana kan lamarin sun nuna damuwa kan yawaitar kashe kashe da satar mutane da yan bindiga yawanci da kayan sojoji ke yi.
Sun yi kira ga rundunar sojojin ta wanke kanta ta hanyar taimakawa yan sanda wurin magance mummunan abin.
Abin da ake zargi ya janyo kisar A cewar The Nation, kisar Ogbolosingha bai zai rasa nasaba da rikicin da ake yi ba tsakanin garin Kalaba/Zarama a yankin wanda ya yi sanadin mutuwar fitattun shugabanni biyu.
An kashe Cif Francis Kolubo, da shugaban kwamitin cigaban unguwa, Cif Samuel Oburo, a watan Yuni saboda zargin cewa sun ki bari a kafa haramtaciyar matatan man a yankin.
Yan sanda sun tabbatar da mutuwar Ogbolosingha Kakakin yan sandan jihar Bayelsa, Asinim Butswat, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa rundunar ta fara bincike.
A wani labarin mai kama wannan, wasu gungun yan bindiga, a safiyar ranar Asabar sun kashe mataimakin shugaba na karamar hukumar Song, Jihar Adamawa, Hon. Ishaya Bakano.
Ana zargin mutuwar Hon Ishaya, wanda ke wakiltar gundumar Gudu Mboi, kisar gilla ne, domin yan bindigan da suka kutsa gidansa da ke Bannga sun tafi jim kadan bayan sun bindige shi har lahira.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Adamawa, Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatarwa Punch Metro afkuwar lamarin.
Source:legithausang