Bayani kan dannau mai danne mutane a barci a mahangar addini da kimiyya.
Shin akwai wata matsala da ka taba samu a lokacin da kake yin barci har ta kai ka ga kasa yin motsi ko magana ko kuma ihu?
Ko kuma ka taɓa ganin wani abu mai kama da inuwa yana gittawa ta gabanka a lokacin da kake cikin barci, ko kuma kakan tsorata?
Masana da dama a fadin duniya na bayyana hakan da dannau, wanda wani yanayi ne da mutum kan riƙa ji amma ba ya iya motsawa a lokacin da ya fara barci.
Idan kuka biyo mu a wannan maƙala za ku fahimci batutuwa da dama game da matsalar barci ta dannau.
Dakta Babagoni Woru, babban daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, ya yi wa BBC karin bayani game da matsalar dannau cewa yakan faru ne musamman a lokacin da mutum yake barci lokacin da ya zo farkawa – wato kamar rabi yana farke kana rabi yana barci.
“A daidai wannan lokacin mutum yakan ji jikinsa babu ƙarfi, kuma zai ji ƙirjinsa gabaki daya ba ya iya motsi, kuma zai ji kamar an danna wani abu yana hana shi numfashi kuma ba ya iya yin magana,” in ji likitan.
Ya ƙara da cewa a wasu lokuta mutum yakan so ya yi magana ko ihu domin ya kuɓutar da kansa amma sai ya kasa.
Sai dai kuma mutane musamman a kasashe masu tasowa da galibi suka fi yin imani da al’ada da addini, kuma ba su yarda ko kuma ba su san wannan yanayi ta fannin kiwon lafiya ba, suna yin camfi a kan dannau, a matsayin wani asiri, ko kuma baƙin-aljani da kan addabi mutum ya hana shi barci.
Malaman addinai da dama musamman na Islama kan bayyana dannau a matsayin wata alama ta shigar shaiɗanu ko baƙaƙen aljanu da ke shafar mutumin da ba ya yin addu’o’i idan zai kwanta.
Malam Hayatu Umarari, wani malamin addinin Musulunci da ke birnin Maiduguri a jihar Bornon Najeriya, ya shaida wa BBC cewa dannau ba wani abu ba ne face shafar aljanu baƙaƙe da kan addabi mutane a lokacin barci.
“Galibi mutanen da ba sa yin addu’o’i kafin su kwanta sun fi samun irin wannan matsala ta dannau.
“Shaiɗanun kan riƙa hawa kansu su danne musu maƙogwaro ko ƙirji, musamman a lokutan sallar asubahi,” in ji shi.
“Yana da kyau duk Musulmi ya riƙa ɗaura alwala ya kuma karanta addu’oi irin su Ayatul Kursiyyu da Falaki da Nasi a ko da yaushe, suna kore duk wani sharrin shaidanu ko aljanu”.
Yadda Dannau kan faruwa ga mutum
Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta WebMD ta Birtaniya ta wallafa bayanan masanan, dannau na faruwa ne a lokacin da mutum ke sauyawa daga matakin ido biyu zuwa barci.
Lokacin wadannan sauye-sauye, mutum zai kasa motsawa ko magana a cikin dakikoki kadan zuwa mintoci kadan.
Masu bincike kan yanayin barci in ji mujallar, sun bayyana cewa a lokuta da dama kasa motsawa a lokacin barci ko kuma dannau, wata alama ce da ke nunawa cewa jiki ba ya motsawa yadda ya kamata a matakai daban-daban na barcin.
Yana da wahala a danganta dannau da manyan matsalolin da suka shafi ƙwaƙwalwa.
Kuma kamar yadda Dakta Babagoni ya yi karin bayani game da yadda matsalar dannau cewa yawanci yakan faru ne a wasu mutane musamman wadanda suke da matsalar barci da ake kira narcolepsy.
“Masu irin wannan matsala ta narcolepsy kan rika yawan barci, kuma barci ba ya isar su saboda matsalar wasu sinadari da ke cikin ƙwaƙwalwarsu, za ka ga ko wane lokaci suna yawan gyangadi ko a wurin aiki ko sana’a,” in ji shi.
Kana kuma in ji likitan akwai wasu nau’ukan mutane da ke fama da matsalar barci da ake kira sleep apnea, da yawanci idan suka kwanta barci suna minshari da matsalar numfashi a lokacin da suke barci su ma suna samun irin wannan matsala ta Dannau.
A cikin ƙarni da dama, akan danganta alamun dannau ta fannoni daban-daban da yawanci aka fi alakantawa da kasancewar “shaidanu” a wuri: baƙaƙen aljanun dare da ba a iya ganinsu a zamanin da
Wasu mutanen in ji masana, sukan rika jin yanayi da shaƙewa a lokacin da suka shiga yanayin dannau.
Dannau ka iya zuwa tare da sauran matsaloli kamar su yawan barci ba a lokacin da ya dace ba, wadda matsala ce da masana suka bayyana cewa kan faru a lokacin da kwakwalwa ta gaza kayyade yanayin barci.
A wadanne lokuta ne yanayin dannau kan faru?
Galibi dannau kan faru sau daya zuwa biyu. Idan hakan ya faru a lokacin da kake jin barci, yanayin dannau ne da ake kira hypnagogic ko kuma predormital.
Idan kuma ya faru a daidai lokacin da kake tashi daga barcin shi ake kira hypnopompic ko postdormital.
A cewar Datkta Babagoni yawanci da sassafe ne aka fi samun matsalar dannau a daidai lokacin da mutum ke tashi daga barci.
“Barcin dan adam ana raba shi kashi biyu, akwai REM wato rapid eye movement wanda lokacin da mutum barci ke nauyi a jikinsa, kuma a wannan lokaci ake mafarki, sai kuma NREM wato non-rapid eye movement wanda shi ne barcin da ba ya tare da mafarki,” in ji shi.
Kana ana sa ran mutum zai yi barci akalla na sa’o’i takwas a ko wace rana kuma yawanci da dare ne.
A lokacin da ake barci mai nauyi mafarkin kan zagayo sau uku ko hudu cikin dare, sai anjima kuma ya yi barci da babu mafarki, to idan aka samu matsala a lokacin wadannan sauye-sauyen a yanayin barci in ji likitan, matsalar dannau na iya faruwa.
“Tsakanin barci da kuma farkawa daga barci a nan ne ake samun dannau ko sleep paralysis,” in ji dakta Goni.
Ya kara da cewa: “A yayin da ka fara barci, jikinka kan rika hutawa sannu a hankali. Galibi kakan kasance cikin rashin sanin abin da ke faruwa, domin haka ba ka sanin sauyin”.
“Amma kuma, idan ka cigaba ko ka san abin da ke faruwa a lokacin da kake fara barcin za ka lura cewa ka kasa motsi ko magana.”
“Lokacin, jikinka ya fara sauyawa tsakanin yanayin barcin (motsawar ido mai sauri) zuwa (motsawar ido marar sauri), irin baccin da ya kan kai tsawon mintoci 90”.
Su wane ne suke kamuwa da matsalar dannau?
Likita Babagoni ya bayyana cewa mutane kusan hudu cikin 10 ka iya samun yanayin dannau.
Kuma yakan samu babba, da yaro, namiji ko mace, da kuma tsofaffi, sannan akan gane irin wannan yanayi daga tsakanin shekaru goma sha uku zuwa sha tara.
“Yakan samu nau’ukan mutanen da ke fama da matsaloli na barci kamar narcplepsy wato yawan barci ko gyangyadi a lokutan da bai dace ba, da kuma sleep apnea da kan samu mutum a lokacin da yake barci wanda kan sa ya rika kasa yin numfashi a yayin da yake tsakiyar barci,”ya ce.
Abubuwan da za a iya dangantawa da dannau:
- Rashin isasshen barci
- Yanayin sauye-sauyen lokacin barci
- Tabuwar kwakwalwa kamar su tsananin damuwa
- Kwanciyar rigingine
- Amfani da wasu ire-iren magunguna
- Shan magugunan ba bisa ka’ida ba.
Shin ana iya magance dannau?
Akasarin mutane ba sa bukatar wani maganin dannau in ji masana, amma ana iya magance matsalolin da suka shafi barci kamar na yawan barci a lokutan da ba su dace ba da kuma tsananin damuwa da ke sa zurfin tunani.
Dakta Babagoni ya bayyana cewa babu wani takamaimen maganain Dannau illa iyaka likitoci kan abubuwan da suka shafi kwakwalwa ko hankalin dan adam su kan bayar da magungunan abubuwan da ke hana barci kamar su tsananin damuwa ko ciwo.
Kana ya ce tsaftace barci na daga cikin abubuwan da mutum zai yi don magance matsalar dannau.
“Yadda ake tsaftace barci shi ne mutum ya zamanto a cikin dakinsa duk wani abu zai iya jan hankali ko kuma hana shi samun ingantaccen barci wajen yain barci, kamar misali in akwai talabijin, ko rediyo, ko hasken fitila duk a kashe,” in ji shi.
Jerin shawarwarin likitoci game da dannau:
- Inganta yanayin barci – kamar tabbatar da cewa ka samu sa’oi shida zuwa takwas na barci a ko wane dare.
- Amfani da magungunan hana damuwa idan likita ya bayar son kayyade lokutan da suka dace a rika barci.
- Magance duk wasu matsaloli da ke damun kwakwalwa da ka iya haifar da matsalar dannau.
- Magance duk wata damuwar barci, kamar su ciwon yawan barci a lokutan da ba su dace ba, ko sankarewar kafa.
- Rage yawan sa rai a cikin duk wata damuwa karama da babba – musamman kafin kwanciyar barci.
- Mutane su gwada kokarin sauya yanayin kwanciya idan suna kwanciya rigingine ne.
- Mutane su tabbatar da sun sanar da likita idan dannau na hana su samun barci mai kyau da dare.
- A rika kwar da duk wani abu da zai dauke hankalin mutum zuwa hana shi samun barci.
- Ya zamanto dakin da mutum yake ana samun iska mai kyau tana shiga ciki.