Bayan ruwan sama, shanu sama da 12 sun mutu a jihar Delta, lamarin da ya jawo kaduwa.
Wasu mazauna sun bayyana yadda suka ji bayan aukuwar lamarin, sun kuma bayyana gargadin da aka yiwa makiyaya .
An rahoto cewa, manoma sun gargadi makiyayan da ke tura shanunsu cikin gonaki a yankin.
An rahoto cewa shanu sama da 12 sun mutu biyo bayan bugun tsawa a garin Urhodo-Ovu na karamar hukumar Ethiope East na jihar Delta, The Nation ta ruwaito.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, makiyayan suna zaune kusa da shanun yayin da aka dauke wasu daga ciki zuwa wani yanki na daji don kiwo lokacin da tsawar ta fado kan shanu sha biyu.
Majiyar ta yi bayanin cewa tsawar ta fado wa shanun ne bayan an dan yi ruwan sama, inda ta kara da cewa ‘yan mintoci kadan sai shanun suka fadi matattu saboda cikinsu ya kumbura.
Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 Hoto: vanguardngr.com Majiyar ta bayyana cewa kashe shanun da tsawar ta yi ya sanya tsoro a zukatan makiyayan wadanda bayan faruwar lamarin suka tsere amma daga baya suka dawo.
An gano cewa kafin ranar da abin ya faru, manoma a lokuta da dama sun gargadi makiyayan da su daina tura shanunsu zuwa gonakin rogonsu amma ba su saurara ba har sai da lamarin ya faru.
Lamarin wanda ya jawo hankalin mutane daga kauyukan da ke makwabtaka da suka bayyana yadda suka ji sun ce har yanzu suna cikin kaduwa game da lamarin, sun kara da cewa wannan zai zama gargadi ga makiyayan da ke daukar shanunsu don lalata gonaki.
READ MORE;Sojoji Sun Kai Samame Maɓuyar IPOB Sun Kama Babban Kwamanda
Dangane da jita-jitar da ake yadawa cewa lamarin na da alaka da bakin jama’a, wata majiyar ta ce irin wannan lamarin ya faru a wasu garuruwa, cewa wannan ba sabon abu bane.
A wani labarin, Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta ce tana adawa da biyan kudin fansa ga ‘yan bidiga don ganin an sako mutanen da aka sace, TheCable ta ruwaito.
Kungiyar kolin ta zamantakewar al’ummar arewa, ta ce tana goyon bayan tattaunawa da ‘yan bindigan. Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na ACF na kasa, ya bayyana matsayin kungiyar a Kaduna ranar Asabar.