Bayan fara yakin Gaza shin me ke faruwa?
Tun Bayan fara yakin Gaza na 7 ga watan Oktoba ne dai Isra’ila ta sauya siyasar ta daga kare kanta zuwa ga kai hare hare ga farar hula a zirin Gaza, sannan ta maida hankalinta kan matakin hukunta fararen hula da nufin yakar sojojin Hamas.
Har ila yau, bisa kididdigar da aka yi, rabin makaman da Isra’ila ta yi amfani da su a yakin, bama-bamai ne marasa lunzami(wanda ba a controling din inda zasu sauka), wanda hakan ya haifar da karuwar kashe fararen hula Falasdinawa.
Gaskiyar yakin Gaza a bayyane yake: mutum miliyan biyu da suka rasa matsugunansu, dubban gidajen da suka ruguje, fiye da 28,000 suka rasa ransu, haka kuma kimanin 70,000 suka jikkata.
A cewar rahotannin hukumomin agaji da hukumomin lafiya a Gaza, kusan kashi 70% na wadanda suka mutu mata ne da kananan yara. Kusan mutum 10,000 da suka ransu yara ne ‘yan kasa da shekaru 18, kuma kusan wasu 8,000 ne suka bace.
A halin da ake ciki , mashigar Rafah, wani karamin gari dake kan iyaka tsakanin Falasdinu da Masar, wanda a da yake da yawan jama’a 300,000, yanzu haka ya zama mafaka ga kusan rabin al’ummar Gaza.
Kafin wannan yakin, al’ummar Zirin Gaza sun kai mutane miliyan 2.2, kuma bayan kwashe mazauna yankin zuwa mashigar Rafah, har yanzu al’ummar wannan yanki na karuwa.
Mazauna Gazan da suka iya stira daga yakin sojojin Isra’ila a yanzu haka suna fuskantar saurin yaduwar cututtuka.
A cikin makonni biyu da suka gabata, cututtuka na numfashi da gudawa a cikin yara ‘yan kasa da shekara biyar sun karu sosai, kuma waɗannan cututtuka sun ci gaba da kama yaranda sukawuce wannan shekarun ma.
Bayan fara yakin 7 ga watan oktoba Faladiwa sun shiga mawuyacin hali
Bugu da kari Netanyahu ya bukaci Biden da ya matsa wa Masar kan ta bude kan iyakokinta da Gaza da kuma karbar ‘yan gudun hijirar Falasdinu.
Wasu daga cikin mambobin majalisar ministocin Isra’ila kuma sun fito fili sun yi magana kan mayar da yankin Zirin Gaza zama maras zaman lafiya ta hanyar lalata matsugunai, gine-gine, makarantu, masallatai da asibitoci gaba daya a Gaza.
Idan kotun kasa da kasa ta tabbatar da shaidar kisan kare dangi, to ita ma Amurka za ta shiga cikin wannan shari’a saboda alakarta da na wannan aikin nasojin Isra’ila, domin a dokokin kasa da kasa, ana daukar wannan mataki a matsayin babban laifi.
Shiga Amurka a cikin wannan lamari ya samo asali ne saboda makaman da take baiwa Isra’ila.
Tun lokacin da aka fara yakin Gaza, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Euro da Mediterranean, Washington ta aika da manyan makamai da harsasai zuwa Isra’ila, wadanda suka hada da bama-bamai 15,000 da kuma turmi 57,000.
Darusa daga barnar dake faruwa a Gaza
Akwai darussa da yawa da za mu koya daga yakin Isra’ila keyi da farar hula a Gaza.
Batu na farko shine ana iya kawar da tsarin soji da sansanonin hama a Gaza, amma wannan ba me yuyuwa bane a iya kankare tunani da fikira ta hamas ba a Gaza.
Abu na karshe kuma shine, batun amfani da tsarin kasashe biyu a Gaza domin kawo karshen rikici tsakanin Isra’ila da Faladinu abu ne wanda ba zai yuwu ba.
Dalili akan hakan kuwa shine gine ginen sabbin matsugunai da Isra’ila tayi a ita kasar ta Falasdinu. Gine ginen da isra’ila ta dinga yi a kasar Falasdinu yana daya daga cikin dalilan da ze jawo yin kasa biyu a gaza yaki faruwa.
A halin yanzu dai masu sa ido kan rikicin na Gaza sun yi ittifaki a kan matsayar cewa, ya kamata a ce samar da kasashe biyu ya zama wani bangare na shawarwarin da ba makawa bayan duk wani yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Shin Isra’ila zata iya gudanar da Al’amuran Gaza bayan kammala yakin da Hamas.
A halin da ake ciki yanzu babu wata gansasshiyar amsa da zata nuna karshen yakin, domin da alama Netanyahu bai shirya kawo karshen yakin ba anan kusa.
Bisa kididdigar da sojojin Isra’ila suka yi, watakila yakin Gaza zai ci gaba har zuwa shekara ta 2024 domin lalata kayayyakin aikin soja na Hamas gaba daya.
Harzi Halevi, kwamandan sojojin Isra’ila, ya yi gargadin cewa: Rashin tsare tsaren yanda za a tafi da zirin Gaza bayan kamala yakin, ze iya rusa duk wata nasara da aka samu.
Barnar da aka yi da kuma yawan hasarar da yakin Gaza ya haifar zai iya raunana tattalin arzikin Isra’ila , tare da karfafa tunanin daukar fansa a tsakanin tsakanin al’umma masu tasowa na Palasdinawa.
Da yawan Falasdiwa, suna ganin martanin da Isra’ila ke yi wa Hamas ta hanyar azabtar da dukkan jama’ar Gaza wani zalunci ne da rashin mutuntaka.
Duk da cewa akwai fargaba da yawa game da matakin na Isra’ila, amma ko shakka babu Hamas ita ce jagorar Falasdinawa kuma ita ke rike da tutar tasu.
A cikin dogon lokaci, gwagwarmayar da aka dade za ta iya haifar da “Hamas ta hada kan al’ummar Gaza da aka yi wa kawanya, da taimakawa wajen wargaza Hukumar Isra’ila, tare da sanya Falasdinawa kallon Hukumar Falasdinu a matsayin wani abu mara amfani ga karfin soja na Isra’ila.”
Duba nan👇👇