Jihar Kaduna- Wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki kan ayarin motocin mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda na shiyya ta 12 da hedikwatarsa da ke Bauchi,
Audu Madaki, inda suka raunata shi tare da kashe daya daga cikin jami’an tsaronsa.
Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, an gano cewa AIG din na kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Bauchi ne wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi wa motarsa kwanton bauna.
An ce lamarin ya faru ne a tsakanin Barde da Jagindi a jihar Kaduna a ranar Talata da misalin karfe 2:30 na rana, Punch ta ruwaito.
Wata majiya a hedikwatar shiyya ta 12 ta shaida cewa an harbi AIG Audu Madaki a yayin harin, yayin da aka harbe jami’in tsaronsa har lahira.
An ce AIG din yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba yayin da aka tsaurara matakan tsaro a kewayen shiyyar.
Wata majiyar kuma ta bayyana cewa an tura jami’an ‘yan sanda dauke da makamai zuwa yankin domin fatattakar ‘yan ta’addan tare da tsaftace dajin.
Jaridar TheCable ta tuntubi Thomas Goni, mai magana da yawun ‘yan sandan shiyya ta 12, don jin ta bakinsa game da lamarin, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan harin ba.
Amma ya yi karin haske da cewa: “Har yanzu muna jiran cikakken bayani kan lamarin.
“Kun san hakan bai faru a yankinmu ba; Hakan ya faru ne a rundunar Kaduna don haka nake kan neman Kaduna don samun cikakkun bayanai daga wurinsu. Karin bayani na nan tafe…
Source:hausalegitng