A wani rahoto da gidan jaridar Leadership Hausa ta wallafa ya nuna a ranar Juma’ar nan ne dubban jama’a suka fito kan titi inda suka zagaye gari da nufin nuna goyon bayansu ga al’umman Palastinu wanda Yahudawa ke zalumta kamar yanda masu gangamin suka bayyana.
Malam Ahmad Yusuf Yashi, wakilin ‘yan uwa musulmai almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na jihar Bauchi ne ya jagoranci masu zagayen garin, ya bayyana cewar sun fito ne domin amsa kiran Ayyatullahi Imam Khumaini na kiran illahirin jama’a da suke amfani da ranar Juma’ar karshen ramadana wajen tunawa da raunanan Palasdinawa da kuma sauran wadanda ake zalumta a fadin duniya.
“Shi wannan massalacin na Quds shi ne masallaci na uku a daraja amma an wayi gari yana karqashin ikon Yahudawan Sahayoniya kuma wajibi ne mu kwato wannan massalacin domin na musulmai ne,” a cewarsa
Ya kuma qara da cewa a irin wannan ranar su na kuma tuna da kuma yin dubiya kan halin da sauran jama’an duniya ke ciki musamman wadanda ake zalumta.
A cewar Ahmad Yashi sun fito ne domin su goyi bayan al’ummar Falastinu tare da tir da zalumcin da Yahudawa ke yi wa al’ummar Falastinuwa, ya nuna cewa shirin Yahudawa ba ga zallar Falastinuwa ya tsaya ba so suke su mamaye yankin Gabas ta tsakiya baki daya.
Ya ce: “Wannan fitowa da muke yi ba ma ga zallar Falastinuwa ba ne, a gaskiyar magana don dukkanin musulman duniya da raunanan da suke rayuwa a doron kasa. Domin da Isra’ila za ta yi nasara kawar da wadanda suke Palastinu to za ta mamaye dukkanin Gabas ta Tsakiya ne, wadannan kasashen irinsu Lebonon, Siriya, Jordan, Yusra da makamantansu. Domin ta taba gwada wannan yunkurin nata a 1967 na mamaye sassan wadannan wuraren.
“Su na nan suna da wannan tunanin da wannan burin. A takaice ma har sun bai wa shirinsu suna da cewa za su samar da Isra’ila babba wanda sun ce za su hada har da Madina daman sun ce Madina kasarsu ce, Annabi da ya zo ne ya koresu a nan.
“Don haka ya kamata musulmai su shiga cikin hayyacinsu ba magana ce ta ‘yan Shi’a ko ‘yan kaza ba. A’a lamari ne da ya shafi musulman duniya baki daya da duk kuma wanda yake da rauni a doron kasa. Kiranmu a nan shi ne al’umma ta zo da Sunnanta da Shi’anta a fito a yi Allah wadai da abun da Yahudawa ke yi a wannan yankin da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu. Kuma insha Allahu nasara na nan tafe ga al’ummar Falastinu,” ya tabbatar.
Wakilin Leadership Hausa da ya kasance da muzaharar ya shaida mana cewar masu muzaharar sun yi ta waken bayyana halin da al’ummar Falasdinawa ke ciki, da kuma nuna goyon bayansu a garesu. An yi zagayen lafiya aka kuma tashi a cikin garin na Bauchi