Basaraken Isolo a Jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka, ya rasu.
Leadership Hausa ta samu labarin cewa Sarkin ya rasu ne jim kadan bayan idar da sallar Idi a ranar Laraba.
Shugaban karamar hukumar Isolo, Olasoju Adebayo, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa za a yi jana’izar marigayin da misalin karfe 4 na yamma.
“Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya umarce ni da na sanar da rasuwar babban basaraken masarautar Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka, Adeola Olushi na III, a yau 10 ga watan Afrilu, 2024. Ya rasu yana da shekaru 64.
“Za a yi jana’izarsa a yau da misalin karfe 4 na yamma a fadarsa, da ke lamba 3/5 a kan titin Akinbaye, Isolo. Allah Ya jikansa ya sa ya huta.”
Sai dai Olasoju bai bayyana dalilin mutuwar basaraken ba.
Basaraken ya shafe shekaru 20 a kan karagar mulki.
A wani labarin na daban shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai don gudanar da aikin gina kasar nan.
A cikin sakonsa na barka da sallah da mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar nan su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.
Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki daya murna, ya kuma yi addu’ar Allah Ya karbi ibadun da aka gabatar.
A cewarsa hanya daya da kasar nan za ta dawo kan turba shi ne cusa kishin kasar a zukatan al’umma.
DUBA NAN: Za’a Iya Kawo Karshen Matsalar Tsaro Inji Tsohon Gwamna
Ya ce hakan zai samu ne idan al’ummar kasar nan suka hade kansu waje daya tare da watsar da bambance.