Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bosso/Paikoro a jihar Neja, Hon. Yusuf Kure Baraje, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen ceto al’ummar mazabarsa daga ayyukan ‘yan fashin daji.
Dan majalisar ya ce halin rashin tsaro da al’ummar mazabarsa ke fuskanta abu ne da ke neman daukar matakin gaggawa domin matsalolin tsaro na kara ta’azzara.
Ya ce, “Misali, a kauyena an kai hare-hare kusan sama da 10, ‘yan fashin har farfajiyata suka shigo suka farmake ni. A yanzu da nake magana da ku, ban taba ganin wani soja da aka tura domin yakar ‘yan fashin dajin a maboyarsu ba.
“Lokaci daya da sojoji suka zo zagayen bincike daga sansaninsu na Kantiri a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna amma babu sojojin da aka jibge a Neja da ke zaune takanas don dakile aniyar ‘yan bindiga.”
Ya nuna takaicinsa kan yadda masu garkuwar ke cin karensu babu babbaka duk kuwa da cewa suna kara jefa jama’a cikin matsin tashin hankali a kowane lokaci.
Ƙazalika ya ce, babu wani yunkuri da sojoji ke yi na ganin bayan ‘yan fashin dajin a halin yanzu.
Baraje ya roki gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yiyuwa domin cimma ‘yan fashin dajin a maboyarsu domin kawo karshen su cikin gaggawa don kauce wa yunkurin ‘yan fashin na share al’ummar kauyukan jihar daga muhallansu.
Source LEADERSHIPHAUSA