An samu rashin jituwa tsakanin iyalin COAS Ibrahim Attahiru da rundunar sojin Najeriya lokacin bankwana da gawar sa.
Iyalansa sun jaddada cewa ba za a birneshi a akwatin gawa ba amma rundunar tace sai an bi al’adar soji.
Da kyar aka shawo kan iyalansa sannan suka amince aka kara fadin kabarinsa yadda akwatin zai shiga An samu karamar hayaniya a ranar Asabar tsakanin iyalan marigayi shugaban sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da rundunar sojin Najeriya yayin birne shi.
Wannan rashin jituwan ne ya kawo jinkirin birne shi domin kuwa iyalansa sun jaddada cewa ba za a birne shi da akwatin gawa ba sai dai yadda addinin Musulunci ya tanadar lokacin da suke bankwana da janaral din.
Amma wasu manyan hafsoshin soji sun jaddada cewa dole ne a birne gawar Attahiru kamar yadda al’adar soji ta tanadar, The Punch ta ruwaito.
Bayan wani lokaci, manyan sojojin sun shawo kan iyalansa kuma an fadada kabarinsa zuwa yadda zai dauka akwatin gawar.
Attahiru da sauran sojoji 10 sun yi hatsarin jirgin sama ne a ranar Juma’a a filin sauka da tashin jiragen sama dake Kaduna.
An gano cewa jirgin dauke da sojoji mai lambar rijista 5N-R203 zai sauka a sansanin dakarun sojin sama dake Mando Kaduna amma ya koma ya sauka a filin jirgin sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau.
Baya ga Attahiru, akwai Birgediya Janar Ahmed Kuliya, O Olayinka da MI Abdulkadir, Manjo N Hamza, Manjo LA Hayat, Sajan O Adesina da Umar. Akwai matukan jirgin OM Oyedepo, TO Asaniyi da AA Olufade.
An dai yi bankwana da gawarwakin sojojin kamar yadda dokar soja ta tanada ba kamar yadda addini ya tanada ba.
A wani labari na daban, sojoji sun rufe yankin da jirgin dakarun sojin saman Najeriya yayi hatsari a ranar Juma’a a filin suaka da tashin jiragen sama na Kaduna.
Jirgin saman wanda ke dauke da shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji ya fadi a filin jirgin inda ya kashe dukkan mutum 11 da ke ciki har da matukan jirgin.
A yayin jawabi kan lamarin, manajan filin jirgin sama na Kaduna, Amina Salami ta sanar da Channels TV cewa hukumar sojin Najeriya sun mamaye yankin da lamarin ya auku.