Emefiele ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi ko bayan cikar wa’adin da CBn ya diba na daina amfani da su.
A yau Talata, 31 ga watan Janairu ne gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele ya gurfana a gaban majalisar wakilai don yi mata bayani kan manufofin CBN.
A ranar 10 ga watan Fabrairu ne wa’adin kwanaki goma da bankin ya kara daina amfani da tsoffin kudi zai cika.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce bankuna za su ci gaba da karbar tsoffin kudi bayan cikar wa’adin da aka duba.
Emefiele ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 31 ga watan Janairu lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai, jaridar The Cable ya rahoto.
Ya ce CBN ma za ta karbi tsoffin kudin daga hannun bankuna bayan cikar wa’adin 10 ga watan Fabrairu.
Emefiele ya yi nuni ga dokar CBN wanda ya wajabtawa babban bankin ci gaba da karbar tsoffin kudi har bayan cikar wa’adin da ya diba na daina amfani da su.
A wata sanarwa da majalisar ta yi a shafinta na twitter ta jaddada matsayin gwamnan babban bankin kasar, inda ta nakalto yana fadin cewa: “Bisa amincewa da shawarar majalisar wakilai da sashi na 20 (3) wanda ya ce ko bayan tsoffin kudin sun rasa martabarsu na halastattun kudi an umurcemu da karbar wadannan kudade.
Source:LegitHausa