Ayman Sejiny babban daraktan gudanarwa na bankin raya ayyukan ci gaba na musulunci ya bayyana cewa, sun saka wadannan kudade a Najeriya da nufin ganin an yi amfani da su wajen bunkasa kananan sana’oi da suka durkushe, ko kuma suka samu koma baya, sakamako bullar cutar corona.
Ya ce bankin yana gudanar da ayyukansa ne a Najeriya bisa yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kansu tare da gwamnatin kasar da kuma sauran bangarori da suke mu’amala da wannan banki, musamman bankin Jaiz, wanda shi ne bankin musulunci a Najeriya.
Tun a cikin shekara ta 2003 ne dai aka kafa bankin Jaiz a Najeriya wanda yake gudanar da ayyukansa bisa ka’idoji na shari’ar musulunci, da suka hada da rashin yin ta’amulli da riba, da kuma kaucewa harkokin kasuwanci da suka shafi abubuwa da aka haramta a muslunci, kamar kasuwancin giya ko abin da ya yi kama da hakan.
A wani labarin na daban majiyoyin kungiyar Taliban sun kungiyar ta kammala kwace iko da jihar Panjshir a kasar Afhanistan, bayan dauki ba dadi da mayakan kungiyar suka yi da magoya bayan Ahmad Mas’ud, wanda yaki mika kai ga kungiyar.
A cikin wani bayani da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi ga mayakan kungiyar a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki a kasar, kuma sun shimfida ikonsu a jihar Panjshir wadda taki mika wuya.
Baya ga haka kuma kungiyar ta nuna hotunan bidiyo na babban ginin gwamnatin jihar Panjshir, inda mayakan kungiyar suka saukar da tutar kasar Afghanistan da ke wurin, suka dora tutarsu.
Sai dai a nasa bangaren Ahmad Mas’ud wanda ke jagorantar mayakan yankin na Panjshir wajen yin turjiya a gaban mayakan Taliban tare da kin mika wuya gare su ya karyata cewa Taliban ta kammala kwace iko da jihar baki daya.
Haka nan kuma ya yi ikirarin cewa, sunan nan cikin jihar kuma za su gaba da yaki da Taliban, kamar yadda ya bukaci al’ummar Afghanistan da su mike su kwaci ‘yancin kansu daga mulkin mallakar Taliban.