An fara mayar da martani game da bidiyon wani mutum da ba a bayyana sunan sa ba wanda aka kama shi a CCTV yana satar kudi a teburin mai kula da hada-hadar kudi a banki, wato kashiya.
Wasu ‘yan Najeriya na cewa barawon ya tafi da kudin ne saboda galibin bankunan Najeriya CCTV din su fanko ce.
Wasu kuma na ganin cewa laifin kashiyan ne, da har mutumin ya samu kwarin gwiwar satar kudin.
Na’urar daukar hoto ta CCTV da ke banki ta nuna wani mutum mai karfin hali da ba’a iya gane shi ba yana satar kudi a teburin kashiya.
Sata Cikin Hikima
A Banki Yadda Wani Barawo Ya Saci Kudi a Banki
Cikin wani fefan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a ranar 29 ga watan Nuwamba, an hangi mutumin yana dibar kudi a teburin Kashiyan bankin.
A Bidiyo Barawon ya saci kudin ne a yayinda Kashiyan ke kokarin sallamar wani kwastoma a cikin bankin
Da suke mayar da martani dangane da bidiyon , yan Najeriya sun bayyana barawon a matsayin mai karfin hali sosai.
Da su ke mayar da martani kan faifan bidiyon, wasu ‘yan Najeriya na cewa barawon yana da wayo ta hanyar da ya dau kudin ba tare da kashiya din ya ganshi ba.
Karanta wasu daga cikin maganganun nasu a kasa:
@Dozzy_Dozzy22 ya ce: “Allah yasa dai ba’a bar mutumin nan ya tsere ba.”
Tayo Henry ya ce: “Ace babu wanda ya kula dashi har ya gama abinda zaiyi?, ai laifin su ne.”
Wani mai amfani da yanar gizo mai suna @stopcorruption1, ya tofa albarkacin bakinsa da :
“Madalla. komai muna yi da gaggawa ba tare da jira ba?
Bankin da ke samun ribar biliyoyin kudi ba zai iya daukar tawagar jami’an tsaro da wanda zasu kula da CCTV?”
@olatee33 yai tambaya: “Jama’a ta ya zan shiga banki nai sata ba tare da an kama ni ba?.”
Wani dan Najeriya ya koka bayan gano abin da ya bata a Najeriya a gonar Landan Legit.ng ta rawaito cewa wani dan Najeriya wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya yi tir da rashin gaskiya da gaskiya da ‘yan Najeriya ke aikatawa tsawon lokaci.
Mutumin ya dauki hotonsa a wata gona a Landan inda ya sayi ƙwai kuma babu kowa a wajen sai kwan da akwatin sa kudin kwan.
Da yake magana da yaren Yarbanci, mutumin ya bukaci ‘yan Najeriya da su sa gaskiya a rayuwar su, ya kara da cewa ta haka ne kakannin mu suka yi rayuwa mai kyau.