Wata kotun majistare da ke zamanta a yankin Igbosere ta yanke wa wani mutum mai suna Dayo Bakare mai shekaru 38 hukuncin daurin shekaru 34 a gidan yari bisa samunsa da laifin yin garkuwa da wata mata ‘yar shekara 27 da haihuwa a shekarar 2012.
Alkalin kotun, Adetokunbo Omoyele, ta yanke wa Bakare hukuncin ne bayan ta same shi da laifukan da ‘yansanda suka tabbatar a kansa.
An gurfanar da wanda ake tuhumar ne a ranar 17 ga Nuwamba, 2012, bisa laifin hada baki, fyade, tsarewa, garkuwa da mutane, kai hari, da kuma yin mummunar illa.
Danssanda mai gabatar da kara, Sufeta Cyriacus Osuji, ya shaida wa kotun cewa Bakare ya hada baki da wasu mutane domin yi wa matar fyade.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Janairu, 2012, da misalin karfe 4 na yamma a wani gida da ke kan titin Akeem Lasisi, Unguwar Shasha a Jihar Legas.
Osuji ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya yi lalata da matar ba bisa ka’ida ba kuma ya tsare ta tsawon sa’o’i takwas.
Ya lura cewa Bakare ya kuma daba wa matar wuka.
Source LEADERSHIPHAUSA