‘Bai kamata malamai su riƙa matsa wa mabiya su zaɓi wani ɗan takara ba’
Yayin da ya rage ƙasa da mako guda a gudanar da babban zaɓen Najeriya, gangamin yaƙin zaɓe na ci gaba da gudana.
Mutane na ƙara bayyana ra’ayinsu game da wanda suke ganin idan an zaɓa zai iya kawo sauyi ga Najeriya, tare da kawo ƙarshen matsalolin da ƙasar ke fuskanta ta fuskoki da dama.
Kan haka malaman manyan addinan ƙasar biyu da suka hada da Kirista da na Musulunci sun fara jan kunnen shugabannin ɓangarorin biyu da su guji katsalandan a harkokin siyasa.
BBC ta tattauna da Rabaran Mato Rataya Masari, wani malamin addinin kirista a jihar Katsina ta arewacin kasar, da kuma Sheikh Sanyinna Babagana Umara Sanda, limamin Juma’a na masallacin Bulunkutu Abuja, a Maiduguri da ke jihar Borno.
Malaman biyu sun shawarci al’umma da su zama masu taka-tsantsan wajen abubuwan da suka shafi zaɓe.
“Kada ‘yan Najeriya su saurari malamai da fasto-fasto da suke fafutukar cewa a zaɓi wani ɗan takara, saboda yawancin su biyan su ake yi su yi hakan,” in ji Rabaran Rataya.
Ya yi zargin cewa ƴan siyasa sun yi amfani da wasu malamai da fasto-fasto wajen tallata kansu, lamarin da ya haifar da ruɗani tsakanin mabiya.
Ya ce “dole mu zaɓi mutumin da ya kamata musamman mu da muke arewa-maso-yamma, inda ba ka isa ka je gona domin yin noma ba. Kullum ba ma barci, babu kuɗi, in ma kana da su daidai kake da maras kuɗi.”
“Duk malaman addinin ko wanne bangare da zai ce ka zaɓi wani domin ƙabilarsa ko addininsa ba ci gaban ƙasa yake nema ba, wataƙila yana cikin irin waɗanda ake biya domin su share wa wani ɗan takara hanya.”
A nasa ɓangaren Sheikh Sanyinna Babagana Umara Sanda ya ce “ya kamata mu ji tsoron Allah da musulmanmu da waɗanda ba musulmanmu ba, fitina na kwance tana barci, Allah ya tsine wa mai tayar da ita, don haka bai kamata wani ya riƙa shirin tayar da ita ba,” in ji Sheik Babagana.
Da aka tambayi Sheik Babaganara’ayinsa game da malaman da suke hawa minbari suna yi wa ‘yan takara kamfe sai ya ce “malami magaji ne ga annabi, idan ka hau minbari kana wa’azi daidai da ka hau shimfiɗar ma’aiki ne kana wa’azi, ba a son a ji son rai ko son zuciya a tare da kai”.
“A matsayinka na malami ba laifi ba ne ka so wani ɗan takara, amma ba daidai ba ne ka kuma ƙaƙabawa mutane shi a zuciya cewa sai sun zaɓe shi”, in ji Malamin.
A siyasar Najeriya ba baƙon abu ba ne amfani da malaman addinai wajen yaƙin neman zaɓe kai-tsaye ko kuma a kaikaice.
A shekarun baya, ana ganin cewa malaman addinai sun taka rawa a yaƙin neman zaɓen ƴan takara a Najeriya, musamman na shugaban ƙasa da na gwamnoni.