Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu wani shirin kwaso ‘yan Nijeriya daga kasar Israila ko kuma Falasdin, domin babu wanda ya bukaci hakan.
Ma’aikatar kula da ‘yan Nijeriya da ke kasashen ketare (NiDCOM), ita ce ta bayyana hakan, inda ta ce ba ta samu wani kiran waya ba daga wani mutum ko kungiya na ‘yan Nijeriya da ke cikin barazana ba game da yakin da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
NIDCOM ta kara da cewa za ta kwaso ‘yan Nijeriya ne kawai idan ta samu kiran waya daga ‘yan Nijeriyan da ke kasashen guda biyu, amma har yanzu ba ta samu hakan ba.
Mai magana da yawun ma’aikatan, Abdur-Rahman Balogun shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dallancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.
Balogun yana mayar da martani ne ga wata tambaya kan ko me gwamnatin tarayya ke yi na kwashe ‘yan Nijeriya mazauna yankunan da ake gwabzawa fada a gabas ta tsakiya.
Dubban ‘yan kasashen waje ne suka makale a Isra’ila da kuma kasar Falasdin, inda ake gwabza kazamin yaki tun bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da hari.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu, kasashe da dama sun kaddamar da ayyukan kwashe ‘yan kasarsu zuwa gida, yayin da wasu ke shirin yin hakan.
Ya zuwa yanzu dai kasashe irinsu Amurka da Jamus da Ukraine da Thailand da Koriya ta Kudu da Austiriya da Brazil da kuma Argentina na daga cikin kasashen da suka mayar da ‘yan kasarsu gida.
Mai magana da yawun NiDCOM ya ce ‘yan wasu kasashe sun yi kiran gaggawa ga gwamnatocinsu na gida don neman taimako, “amma ba mu samu ko kira daya daga ‘yan kasarmu da ke yankunan guda biyu ba.”
Ya tunatar da cewa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce ’yan Nijeriya mazauna kasashen waje ba sa fuskantar matsin lamba saboda yakin da ake yi a zirin Gaza.
A cewarsa, ma’aikatar za ta iya yin aiki ne kawai idan ta sami kiran gaggawa daga mutanen da ke cikin kasashe masu fama da rikici.
Ya kara da cewa a lokacin da NiDCOM da sauran hukumomin da abin ya shafab a kasar suka samu kiran gaggawa daga ‘yan Nijeriya mazauna kasar Sin, a lokacin barkewar cutar Korona, da kuma na yakin Ukraine da Sudan lokacin da yakin ya barke a yankunan, “mun amsa kuma da yawa daga cikin ‘yan kasarmu mun mayar da su gida.”
Sojojin Isra’ila sun umurci sama da mutane miliyan daya da su fice daga arewacin Gaza cikin sa’o’i 24 gabanin wani samame da sojoji ke shirin kaiwa.
Kusan ‘yan Falasdin 5,100 ne aka kashe a Zirin Gaza tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai a yankin da ta mamaye bayan harin da Hamas ta kai a cikin Isra’ila fiye da makonni biyu da suka wuce.
Source LEADERSHIPHAUSA