Daga Comr Abba Sani Pantami
Idan baku manta ba a watan December na shekarar da ta gabata ba, Buba Galadima yasha alwashin cewa matukar shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya saka hannu a sabuwar dokar hukumar zabe ta INEC to a fille mishi kai.
A jiya Jumma’a shugaba Buhari ya sanya hannu a sabuwar dokar, wanda hakan ya jawo cece-kuce tare da tofa albarkacin baki kan tutiyan da Buba Galadima yayi matukar shugaban kasar ya sanya hannu, inda har wasu suke kira da a gaggauta fillewa Buba Galadima kai.
A jiya da dare manema labarai suka tuntubi Buba Galadima domin suji ta bakinshi kan tutiyar da yayi, inda Buba Galadima ya shaidawa manema labarai cewa akwai dan gyare gyare da aka yi akan dokar sabanin lokacin da yayi tutiya akan cewa shugaban bazai iya saka hannu ba.
Buba Galadima yace ‘yan Najeriya basa nutsuwa su fahimci mutum kawai sai su dinga yanke mishi hukunci ido rufe.
Buba Galadima ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya fille mishi kai saboda ba don Allah shugaban ya saka hannu ba, kuma akwai gyare gyare da shugaban yake so a yi a ciki duk da ya saka hannun.
Masu karatu me zakuce?