Daya cikin yan ta’addan da suke rike da fasinjojin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja ya yi barazanar cewa babu makawa za su tarwatsa Najeriya.
Dan ta’addan wanda ya yi ikirarin cewa yana daga cikin wadanda suke tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja ya ce yana neman Shugaba Buhari da El-Rufai don ya kashe su.
Yan ta’addan sun ce su aikin Allah suke yi kuma sun yi imanin cewa Allah yana tare da su kuma ba za su fara ba sai sun cimma nasarar tarwatsa kasar.
Daya cikin yan ta’addan da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja yayin harin da aka kai a ranar 5 ga watan Yulin 2022 ya yi barazanar tarwatsa Najeriya, rahoton Daily Trust.
Daily Trust ta rahoto yadda wadanda suka sace fasinjojin jirgin suka yi murna bayan ISWAP ta kai hari a Kuje ta saki fursunoni fiye da 800 ciki har da yan ta’adda da ke tsare.
Yan ta’adda, tunda farko sun bukaci a saki wasu yaransu da kwamandojinsu a matsayin sharadi na sakin wasu fasinjojin.
Sun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya amma tun bayan harin gidan yarin, tattaunawar ta dauki sabon salo.
A wani bidiyo mai tada hankali da yan ta’addan suka fitar, an ga wani fursuna da ya ce ya tsere daga Kuje sanye da kayan sojoji da bindiga da harsashi.
Ya bayyana wadanda aka sace din a matsayin ‘datti’ da aka so yin amfani da su don samun yancinsa.
Da ya ke magana ga shugaban kasa, ya ce: “Dole sai mun tarwatsa kasar, idan kana so ka bi addinin gaskiya, ka zo ka yi hakan amma ba za mu fasa ba.
Ka sani dole za mu kamo ka kuma mu kawo ka daji mu yanka ka tare da El-Rufai.
Ka kalle ni, kun aika hotuna na ko ina domin mutane su kama ni amma nima ina sanarwa duk wanda ya gan ku (Buhari da El-Rufai) ya kawo min ku, don in kashe.”
Source:legithausang