Babban lauya, Babatunde Ogala ya yi bayanin abin da dokar kasa da tsarin mulki suka ce a game da takara.
Babban Lauyan ya ce babu ruwan kundin tsarin mulki da addini wajen tsaida takara a Najeriya Ogala ya kare Tinubu, yana ganin kamata ya yi a yabawa ‘Dan takaran na APC, ba a kushe shi ba Abuja.
A karon farko a cikin shekaru kusan 30, babbar jam’iyyar siyasa a Najeriya ta zabi ‘yan takararta na zaben shugaban kasa duk su zama Musulmai.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Babatunde Ogala wanda Lauya ne wanda ya kai matsayin SAN a Najeriya, ya tsoma baki a kan takarar APC a zaben 2023.
Babatunde Ogala SAN yake cewa Bola Ahmed Tinubu bai saba wata doka saboda ya zabi Musulmi ya zama abokin takararsa, duk da shi yana Musulmin ba.
Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, Ogala ya kare Mai gidansa a game da daukar Musulmi da ya yi, ya jawo tikitin Musulmi-Musulmi.
Ogala shi ne shugaban sashen shari’a na kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a 2023, ya kuma yi karin-haske a kan abin da tsarin mulki ya ce.
“Tinubu ya yi wani abin da ya sabawa damar da doka ta ba shi wajen daukar abokin takara? Dole mu komawa sashe na 14 da 15 na dokar kasa.”
”Dokar ta yi maganar adalci da gaskiya wajen rabon dukiyar kasa, amma ba ta kawo batun addini ba. “Dokar ta yi bayanin bambance-bambane da wakilcin al’umma. Tsarin mulki bai yi batun addini ba, saboda haka ba zai yiwu ace an ware wasu ba.”
Babatunde Ogala SAN Rahoton yake cewa Ogala ya nemi a yabawa ‘dan takaran shugaban kasar na APC ne saboda ya duako mutum daga yankin da ba su da rinjaye a siyasar kasar.
“Mu na da manyan kabilu uku a Najeriya – Hausa/Fulani, Yarbawa da Ibo.
Mu na lura da marasa rinjaye, irinsu Kashim Shetimma – Kanuri daga Borno? Babban lauyan yake cewa kowace jam’iyya ta fito lashe zaben 2023 ne, wannan ya sa dole ‘dan takara ya yi duk abin da zai taimaka masa wajen yin nasara.
APC ta yi kokarin ba ‘Dan Kudu tikiti a zaben 2023, abin da PDP ta gagara yi, inji Ogala wanda yake sa ran cewa Sanata Kashim zai kai jam’iyyar ga cin zabe.
Gwamnonin APC sun hadu a Daura Kun samu labari Gwamnoni sun nuna rashin jin dadin yadda Bola Tinubu ya dauko abokin takarara.
Hakan ta sa Gwamnonin su ka yi zama da Shugaban kasa.
Daga baya Shugaba Muhammadu Buhari ya lallashi Gwamnonin jam’iyyarsa, a karshe suka amince Kashim Shettima ya rike tutar jam’iyyar APC mai mulki.
Source:Hausalegitng