Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta shirya liyafar bankwana ta girmamawa ga tsohon shugabanta, CGI Muhammad Babandede.
An gudanar da liyafar ce a ranar Juma’a 10 ga Satumbar 2021, sakamakon ritayar da ya yi daga aiki bayan shafe shekara 31 yana aiki a hukumar.
An naɗa Babandede ne a shugabancin hukumar a shekarar 2015, inda ya karɓi ragama daga hannun CGI Martin Kure Abeshi.
Babandede shi ne shugaban hukumar na 16, wanda ya shafe shafe shekaru biyar da watanni yana shugabanci. Ya samu nasorori da dama wanda daga ciki ya yi matuƙar ƙoƙarin zamanantar da ayyukan hukumar.
Shi dai tsohon shugaban Hukumar NIS, Muhammad Babandede ya kawo sauye-sauye da dama a hukumar da suka haɗa da mayar da fasfo na Nijeriya zuwa na zamani ta na’ura, sauƙaƙa hanyoyin bayar da shi da kuma ɓullo da shirin bayar da biza yayin shigowa ƙasar nan. Haka kuma ya ƙawata shalkwatar hukumar tare da samar da cibiyoyin tattara bayanai daga dukkanin iyakokin Nijeriya.
Da yake gabatar da jawabin bankwana a wajen taron, Babandede ya bayyana cewa yana matuƙar farin ciki zai bar hukumar a turbar ci gaba fiye da yadda ya sameta.Ya kuma yaba wa jami’an hukumar musamman waɗanda suka yi aiki tare da kuma waɗanda suka bayar da shawarwari na ciki da wajen hukumar.
Ya ce waɗannan nasarori da hukumar ta samu a ƙarƙashin shugabancinsa, ba shi kaɗai ne ya samar ba, ya samu ne sakamakon haɗin kai da goyan baya da jami’an suka ba shi.
“Ina roƙon dukkan jami’an da na sama musu lokacin gudanar da aiki su yafe min, ni ma na yafe wa dukkan waɗanda suka yi min laifi, domin dole ne sai na saɓa wa wani, kuma dole ne wani ya saɓa min, wannan ne ya sa nake roƙon yafiya kamar yadda addinin Musulunci ya shar’anta.”
Babandede ya kuma yi alƙawarin zai ci gaba da kasancewa jakadan hukumar tare da alƙawarin bayar da gudummawa a duk lokacin da aka buƙaci hakan. Ya kuma nuna godiyarsa ga Minista Rauf Aregbesola wanda ya sanya wa babbar cibiyar taro ta hukumar sunansa.
Shi ma sabon muƙaddashin Hukumar NIS, Idris Isa Jere ya yaba da ayyukan da tsohon shugaban ya gudanar na shekaru biyar da ya yi yana shugabanci. Ya jinjina masa tare da yi masa fatan alkairi a dukkan harkokin da zai sa gaba.
Jim kaɗan bayan miƙa masa ragamar shugabancin hukumar, Isa Jere ya gudanar da ganawar sirri da jami’an hukumar domin samun goyan bayansu wajen tafiyartar da hukumar ta hanyar da ta dace.
Daga cikin jami’an da suka halarci taron, wasu sun fashe da kuka lokacin da tsohon shugaban yake gabatar da jawabin.
Mahalarta taron sun haɗa da manyan jami’an Hukumar NIS da iyalan tsohon shugabanta da ‘yan’uwa da abokan arzikin da ‘yan jarida.