Tsohon kwaminshinan addinan Jihar Kano, Dr Tahar Baba Impossible ya bayyana a wani faifan bidiyo da gidan rediyon Freedom Radio ta saki a channel din ta yootube yana bayyana cewa da bukatar malamai su bara dangane da wata magana.
Baba Impossible ya bayyana cewa da bukatar malamai musaman wadanda aka kira da coaliation of ulama su fito idan kuma ba haka to dda wata manufa a ciki.
Tun da farko tsohon kwamishinan ya bayyana cewa wannan ba wani abin cece kuce bane, ya kuma bayyana cewa ya kamata a tsaya a kalli wannan magana domin wannan tsabar sakin baki ne ga darajar manzo sallalahu alaihi wasallama.
Cikin alamun takaici Baba Impossible ya bayyana cewa kalma biyu da aka fada tayi nauyi, ya kuma bayyana daya bazai iya fadar ta ba saboda tayi nauyi amma ya bayyana wacce yace “Shi baya bukatar taimakon manzon Allah s.a.w.w”
Baba Impossible ya bayyana cewa, duk kasar nan sai da ta taru lokacin da aka ce Malam Abduljabbar yayi irin wadannan maganganu.
Baba Impossible ya bayyana cewa daga karshe wata kungiya da ake kira da coalation suka shiga gaba aka tafi kotu kuma a ka tabbatar anyi hukunci
Baba Impossible ya sanar da malamai cewa, wadanda suka dunkule suka yaki Malam Abduljabbar a kan cewa ya zagi manzo Allah, “Babu shakka wannan ya zagi manzo”
Baba Impossible bai kama suna ba amma ga dukkan alamu ana ganin yana magana a kan wani malamin kungiyar wahabiyawa ne a garin Bauchi mai suna Ustaz Idris.
Sheikh Dakta Abduljabbar Nasiru kabara dai na zaman gidan yari sakamakon hukuncin kisa da wata kotu a jihar kano ranar 15 ga watan disambar shekarar data gabata ta yanke masa.
Baba Impossible dai shine kwamishinan addinai na wancan lokaci da aka yankewa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin na kisa, kuma yayi aiki kafada da kafada da kungiyar “Coaliation of Ulama” kafin daga baya gwamnati ta sanar da korar shi daga mukamin sa.