‘Ba wanda zai fada mini wani abu a game da siyasar Jigawa’
Dan takarar gwamnan jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Malam Aminu Ibrahim Ringim, ya bayyana cewa shi a ganinsa babu wanda zai fada masa wani abu kan harkar siyasar Jigawa.
A cikin wata hira da ya yi da BBC, ya ce ya fara siyasa a jihar ne tun a 1976, da shi aka yi aikin da ya kafa kananan hukumomi a kasar.
Ya ce ”Na je majalisar tarayyar a 1983, na je Legas, na san abin da nayi a zamanin PRP, na dawo na yi ANPP na yi UNCP, sannan na dawo na yi PDP, kowanne aka kafa da ni aka kafa shi, APC ce kawai ba a kafata da ni ba.”
Dan takarar gwamnan a jam’iyyar ta NNPP, ya ce duk abin da zai fada an san abin da yake nufi.
Don haka idan dai batu ne na siyasa ko saninta a jihar Jigawa sai dai a daga masa kafa in ji shi.
Malam Aminu Ringim ya ce don ya fito takara a sabuwar jam’iyya ba ya nufin ya ci baya bane, abin da yake so mutane su gane a game da jam’iyya shi ne kowacce manufa jam’iyya ta fito da ita, to aiwatar da ita shi ne abu muhimmi.
Dan takarar gwamnan ya ce, ”Mu abin da yake tsarin cikin tafiyarmu shi ne yau a Najeriya abin da ake magana a kai shi ne kasarmu babu tsaro, sannan yau a kasarmu akwai talauci ga rashin aikin yi, to dukkan wadannan abubuwa sune abin da za mu mayar da hankalinmu a kai.”
Ya ce, ‘’Jihar Jigawa a yanzu na bukatar a fitar ma ta da hanyoyin da bakin kudi za su rika shigo ma ta ba iya na gwamnati ba.”
Malam Aminu Ringim ya kara da cewa don ya fito takara fiye da sau daya bai ci zabe ba, ba wani abu ba ne don a tarihin jihar Jigawa babu wanda ya yi takara sau daya ya samu nasara in ban da Ibrahim Saminu Turaki, sai kuma kila Ali Sa’adu a wancan lokacin.
Dan takarar gwamnan ya ce, batun wai yadda za su tunkari manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu wato APC da PDP, shi wannan ba abin damuwa ba ne. Ya ce, ”Batun wai ya zamu tunkari sauran jam’iyyu, ai sai dai a ce ya za a yi su su tunkaremu? Su sun sani, mu mun sani, sannan kowa ya sani a jihar Jigawa, in dai ana maganar magoyin baya mai zabe ba a na maganar ko yaya ba, to kuwa kowaye sai dai a ce ya zai yi ya tunkaremu?”
Kuma a bari mu kama aikin a gani ya zamu yi, in ji shi.
A Jigawa, kamar sauran jihohin Najeriya, hukumar zabe ta INEC ta kafe sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen gwamna.
Kusan a iya cewa wannan ne karon farko a tarihin jihar, da aka samu manyan ‘yan takarar da a ke ganin mafi yawansu na da ɗumbin magoya baya.