Ba ma goyon bayan dakatar da Sheikh Nuru Khalid – Malamai.
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Izala a Najeriya (mai hedkwata a Jos), Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce ba ya goyon bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Nuru Khalid, limamin Masallacin Apo da ke Abuja.
Ya ce idan har malamin ya yi ba daidai ba, kamata ya yi a kai korafi a gaban majalisar malamai da ke Abuja. Sai dai ba kwamitin masallaci ya dauki matakin dakatar da shi kai-tsaye ba.
“Don ita majalisar malamai ta zauna da shi, ta duba damuwar. Idan abin da ya shafi a yi mai nasiha ne, sai a yi masa nasiha. Idan wanda ya shafi a yi masa gargadi ne, a yi masa… ko idan abin da ya shafi dakatarwa ne na dan wani lokaci, sai a yi masa,” in ji Shekih Sambo.
Hakazalika shi ma wani malamin addini a Abuja, Malam Rashid bn Al-Qasim (Asadul Islam) ya ce duk da cewa yana da bambancin ra’ayi tsakaninsa da Sheikh Nuru Khalid amma a cewarsa ba a yi malamin adalci ba.
“Duka maganganunsa dari bisa dari gaskiya ne,” in ji Malam Rashid kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
A ranar Asabar ne kwamitin Masallacin Apo ya sanar da dakatar da Sheikh Nuru Khalid bayan wata huduba da ya yi ranar Juma’a, wadda a cikinta ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya.