Ba a samu sauyin shugabancin jam’iyya ba – APC.
Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an samu sauyin shugabanci a cikinta.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun sakatarenta John James Akpanudoedehe.
Sanarwar ta ce: “An ja hankalinmu jan wasu rahotanni da wasu kaffen yaɗa labarai suka wallafa cewa an sauya shugabancin jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta ce wannan labarai da jaridu suke yaɗawa na ƙanzon kurge ne marar tushe.
Tun da fari dai a ranar Litinin ne jaridar Thisday ta ruwaito cewa ana zargin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cire gwamnan Yobe Mai Mala Buni, a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Rahoton na Thisday ya kuma ce shugaban ƙasar ya yi umarnin maye gurbin Buni da takwaransa na jihar Neja Abubakar Sani Bello.
Rahoton ya kuma ce wani ɓangare na gwamnonin APC sun yi ƙorafi sosai ga shugaban ƙasar cewa Buni ba ya son a gudanar da babban taron jam’iyyar kamar yadda aka tsara, sabida babu wasu shirye-shirye da aka gudanar zuwa yanzu.
A kan hakan ne sai shugaban ƙasar ya ba da umarnin gaggawa cewa a cire Buni tare da saka sabon shugaba, duk dai a ta bakin jaridar Thisday.
A cikin sanarwar tata, APC ta ce “muna kira ga ɗumbin magoya bayanmu da mambobinmu da dukkan al’umma cewa su kwantar da hankalinsu tare da bai wa Gwamna Mai Mala Buni mai shugabantar APC goyon baya, don a samu a gudanar da babban taron jam’iyya marar maguɗi.