Ayatullah Ramezani, babban shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Bait (a.s) wanda ya yi tafiya zuwa nahiyar Afirka domin halartar tarukan maulidin manzon Allah da Imam Sadik (AS), ya samu halartar taron rukunin wasu musulmi masu fafutukar mata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, A cikin wannan taro, yayin da yake ishara da irin rawar da mata ke takawa wajen raya zuriya, ya ce: Musulunci bai ce mata su zauna a gida kawai ba, duk da cewa ayyukan gida ma suna da nasu rawar da su ke takawa.
Babban shugaban majalisar duniya ta Ahlul-Bait (a.s), ya jaddada matsayin mata musulmi a cikin al’umma, ya kuma bayyana cewa: Mata a duniya an yi watsi da su (ana nuna rashin darajarsu), da cewa za ku iya mayar da martani kan wadannan matsaloli da samar da zamantakewa a kungiyance da zai taimaka wannan tsari.
Ya ce ya zama wajibi a inganta ilimin mata musulmi sannan ya yi jawabi ga mahalarta taron da cewa: ku taka rawar ilimi da ci gaba a cikin al’ummar ku tare da kara karatunku domin ku kara samun sani ga irin rawar da kuke takawa.
Source: ABNA