Shuwagabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirca AU zasu gudanar da taro a karshen wannan makon don tattauna batutuwa da dama kuma masu muhimmanci.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban harkokin gudanarwa na kungiyar Moussa Faki Mahamat yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa batutuwan da za’a tattauna sun hada da juye-juyen mulki da suka kama daga Sudan har zuwa yankin Sahel da wasu kasashen yammacin Afirca.
Har’ila yau akwai batun Cutar Covid 19 da kuma batun bawa haramtacciyar kasar Isra’ila mamba mai sa ido a kungiyar ba tare da tuntubar shuwagabannin kasashen ba. Labarin ya kara da cewa kasashen Najeriya, Aljeriya, Afirca da Kudu da dukkan kasashen kudancin nahiyar suna adawa da samuwar Isra’ila a cikin kungiyar. Sai dai Democradiyyar Congo, Gabon, Morocco da Togo suna gayon bayan Isra’ela.