Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi tafiya zuwa Turai a daren Litinin da ya gabata.
Rohotanni sun bayyana yadda Atiku ya yi tafiyar don neman lafiyarsa, duk da dai kakakinsa, Paul Ibe ya musanta hakan.
Atiku da Asiwaju Bola Tinubu sun samu damar ganawa a Turai duk da kasancewarsu manyan abokan adawa a zaben shekara mai zuwa.
‘Dan Takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi tafiya zuwa kasar Turai.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bar kasar ne bayan ya gana da Asiwaju Bola Tinubu, ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC, a filin sauka da tashin jiragen Nnamdi Azikiwe dake Abuja, Daily Trust ta rahoto.
An samu rahotannin dake bayyana yadda ‘dan takarar jam’iyyar PDP ya bar kasar don neman lafiyarsa, amma sai dai Paul Ibe, mai magana da yawunsa, ya musanta hakan, tare da cewa Atiku ya yi tafiyar ne don kasuwanci.
“Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fita kasar waje a daren jiya tare da abokan kasuwancinsa na daya daga cikin kasuwancinsa da ta samu tangarda saboda kullen Oktoba da rushewar tattalin arziki.”
“Taron zai maida hankali ne wajen neman mafita akan yadda za’a bunkasa kayayyakin da kasuwancin da ake samarwa,” a cewar Ibe a wata takarda.
Kakakin bai bayyana takamaiman kasar da Atiku ya je ba. ‘Dan takarar yayi watsi da kamfen dinsa a jihar Akwa Ibom a makon da ya gabata, gami da garzayawa zuwa Kaduna a ranar Litinin.
‘Yan daba sun kaiwa magoya bayansa hari a wajen zagaye, wanda yayi matukar bata masa rai, hakan yasa yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi jan kunne ga sauran jam’iyyu da magoya bayansu da su tabbatar da zaman lafiya.
Yayin da Atiku ya aje kamfen dinsa, daya daga cikin manyan abokan adawarsa na zaben shekara mai zuwa Tinubu na Turai.
PDP sun amfani da hakan a matsayin abun magana, inda suke cewa rashin ‘dan takarar jam’iyya mai mulkin a kasar na nuna bai shirya jagorancin ba.
A wani labari na daban, a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ya saki burikansa biyar wadanda ya ke son cikawa da zarar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Ya saki kudirorin nasa guda biyar ne ta shafinsa na Twitter yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP a karshen makon nan.
Source:legithausang