Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nada Sanata Dino Melaye da Dakta Daniel Bwala a matasayin masu magana da yawunsa a yakin zaben shugaban
kasa da ke tafe a 2023.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a sanarwar da mai bashi shawara a bangaren yada labarai, Mr Paul Ibe ya sanya wa hanun aka kuma traba wa manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ya kuma ce, nadin ya fara aiki ne a nan take.
Za Mu Ceto Zamfara, In Ji Atiku Yayin Da Ya Amshi Baƙuncin Dauda Lawal
Dinol Malaye, wanda dan garin Ayetoro Gbede da ke karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, ya kuma wakilci mazabar kogi ta yamma a majalisar daddatawa ta 8.
Daniel Bwala, kuwa ya fito ne daga Jihar Adamawa, ya kuma kasance kwarraren lauye ne kafin wannan nadin.
A wani labarin na daban jam’iyyar APC ta sanar da nada gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Lalong, a matsayin daraktan gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2023 da ke tafe.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da yake hira da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa jim-kadan bayan sun yi wata ganawa da shugaba, Muhammadu Buhari, a Villa da ke Abuja.
Tinubu Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba, Ya Tsufa, Cewar Surukinsa Tee Mac
Adamu wanda ya samu rakiyar dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin dan takarar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da shi kansa gwamnan Jihar na Filato, Lalong
Source: legithausang