Atiku da gwamnonin PDP na shirin lallashin Gwamna Wike.
Babbar jam’iyar adawa a Najeriya PDP ta umarci kwamitin da ta kafa don lallashin gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya roƙe shi, don ci gaba da zama a jam’iyyar.
Tun lokacin da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya zabi gwamnan Delta Ifeanyi Okowa maimakon gwamnan na Rivers a matsayin mataimakinsa ne aka fara samun takun saƙa da Wike da wasu gwamnoni da ke goya masa baya.
Sai dai shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin, ya shaida wa ‘yan jarida cewa akwai ƙwarin gwiwar cewa Wiken zai ci gaba da zama a PDP.
A halin da ake ciki dai an kafa wani kwamiti mai mutum tara, wanda aka ɗora wa alhakin sasanta ɓangarorin biyu.
A sanarwar da Walid Jibrin ya fitar ranar Lahadi da marece, ya ce mambobin kwamitin sun haɗa da Atiku Abubakar da gwamnonin PDP na jihohi 13.
Sanata Jibril ya ce mambobin kwamitin za su kai wa Wike ziyara da zarar Atiku da shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu sun koma Najeriya daga hutun da suke yi. Wasu rahotanni dai sun ce gwamnan ya ƙi yarda ya gana da wasu gaggan jam’iyyar PDP da ke da kusanci da Atiku, don sasanta su.
Su ma wasu muƙarraban Gwamna Wike da a halin yanzu ke nuna damuwa da halin da ake ciki a jam’iyyar, sun dage kan cewa dole ne Atiku ya ajiye Okowa ya dauki Wike idan yana son a sasanta.
Manyan jam’iyyar PDP kamar tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose, da kuma gwamnan Benue Samuel Ortom, da tsohon gwamnan Plateau Jona Jang na cikin wadanda suka yi Allah-wadai da zaɓar Okowa a matsayin mataimakin Atiku. Akwai ‘yan jam’iyyar PDP da dama da ke ganin cewa Wike bai cancanci abun da suke gani a matsayin ‘cin kashin’ da ake yi masa a jam’iyyar PDP ba, saboda yadda ya tsaya kai da fata a jam’iyyar tun kafa ta ba tare da ya taba sauya sheka ba.
Sai dai a lokaci guda wasu na da ra’ayin cewa ya yi takara da Atiku, har ma ya kalubalance shi a bangarori da dama, don haka ba abun mamaki ba ne idan Atiku ya zabi wanda zai fi sakin jiki ya yi aiki tare da shi.
A can baya an taba samun dambarwa tsakanin shugaban Najeriya da mataimakinsa lokacin Obasanjo da Atiku, abin da ake ganin ya riƙa mayar da hannun agogo baya wajen kawo ci gaba.