Ba wannan ne karon farko da aka ji Shugaban kasar zai yi zama irin wannan a Aso Rock Villa ba.
Taron ya biyo bayan barazanar da ‘Yan Majalisar Dattawa suke yi na tunbuke Shugaban Najeriyan.
Sa’o’i kadan bayan Sanatoci sun yi barazanar tunbuke Muhammadu Buhari daga kan mulki, sai aka ji shugaban kasa ya kira wani taro na gaggawa a Aso Villa.
Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya gayyaci shugabannin jami’an tsaro da hafsoshi zuwa taron musamman da za ayi a yau dinnan.
Ana sa rai za ayi wannan zama ne a Aso Villa kuma za’ayi zaman da da shugabannin sojoji; hafsun sojojin kasa, Janar Faruk Yahaya, hafsun sojojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Haka zalika akwai hafsun sojojin sama, AVM Isiaka Oladayo Amao, da hafsun tsaro na kasa baki daya, Janar Lucky Irabor da Sufetan ‘Yan Sanda, Usman Baba.
Za ayi wannan zama ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli 2022 a fadar Aso Villa da ke Abuja.
A zaman da majalisar dattawa tayi a jiya, an bijiro da maganar tunbuke Mai girma shugaban kasa muddin gwamnati ta gagara magance matslar tsaro a kasar.
Martanin Lai Mohammed Bayan wannan magana da aka kawo a majalisar, gwamnatin tarayya ta fito ta maida martani.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya yi magana bayan taron FEC da aka yi a fadar shugaban kasa, yace gwamnati na bakin kokarinta a kan batun.
Alhaji Mohammed ya yabi Sanatocin saboda yadda suka nuna damuwarsu a game da sha’anin tsaro, yace gwamnati na yunkurin ganin an tsare rayuka da dukiyoyi.
Rahoton yace Sanatoci sun yi niyyar a bijiro da muhawara a kan sauke shugaban kasa. Amma shugaban majalisa, Dr. Ahmad Lawan bai bada wannan damar ba.
Wa’adin Majalisar Dattawa Sanata Philip Aduda ya fara kawo maganar, yace akwai bukatar Majalisa ta ba shugaban Najeriya wa’adin makonni shida domin ya yi maganin ta’addanci a kasar.
Kamar yadda kuka samu labari, hakan na zuwa ne biyo bayan yawaitar ta’addancin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda wasu a sassa musamman na Arewacin ƙasar nan.
Source:hausalegitng