An girke jami’an tsaro a sakateriyar APC yayin da ake sa ran Asiwaju Tinubu da Shettima za su kai ziyara.
Asiwaju Tinubu da Shettima za su kai ziyarar ne ta farko tun bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar.
A ranar 28 ga watan nan ne za a fara gangamin kamfen din ‘yan takarar shugaban kasa, kowacce jam’iyya na shiri.
Dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima za su kai ziyara sakateriyar jam’iyyar APC a yau Laraba, 7 ga watan Satumba, Punch ta ruwaito.
Rahoton da muke samu ya ce, tuni an girke jami’an tsaro ta kowacce kofa da sakon sakateriyar a shirye-shiryen karbar jiga-jigan na APC.
An ga motocin sintiri da dama a zagaye da sakateriyar manyan jami’ai dake kai komo a zagayenta.
An ce Tinubu da Shettima za su halarci wata ganawar wucin gadi ne da kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa a sakatariyar da misalin karfe 10:00 na safe.
Wannan na zuwa ne bayan watanni uku da Tinubu ya dage kai ziyarar farko ga sakatariyar bayan lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa da aka a APC.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar APC, majiya ta ce ganawar za ta ba da damar tattaunawa kan shirin kamfen din Tinubu da kuma sake fasalin tsarin shi kansa kamfen din da za a fara a ranar 28 ga watan nan.
Hakazalika, majiyar ta kuma kara da cewam za a takaita adadin wadanda za su shiga cikin sakatariyar domin rage cunkoson jama’a da kuma wasu dalilai na tsaro.
Ana sa ran Tinubu da Shettima su yiwa manema labarai bayani a sakateriyar jam’iyyar ta APC bayan kammala ganawar.
Source: LEGITHAUSA