Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi rikicin masarautar Kano.
Babbar kotun tarayya da ke Kano, karkashin jagorancin mai shari’a S. A. Amobeda, ta bayar da umarnin korar Sarkin Muhammadu Sanusi na II daga fadar Kofar Kudu, tare da dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
A gefe guda kuma babbar kotun Jihar Kano, ta bayar da umarnin hana fitar da Sarki Sanusi II daga fadar masarautar Kano.
Umarnin da kotunan biyu suka bayar ya haifar da ruɗani da rashin tabbas kan harkokin shari’a a jihar.
A wani labarin na daban majalisar Dattawa ta amince da dokar dawo da tsohon taken kasar nan, a wani yunkuri na dabbaka kishi a zukatan ‘yan Nijeriya.
Sai dai wasu ‘yan majalisar sun nuna takaicinsu kan wannan mataki da majalisar ta dauka.
Wannan doka ce da ‘yan majalisar suka ba ta muhimmanci da kuma hanzarta amincewa da ita a cikin kwanaki biyu kacal,
Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Okpeyemi Bamidele ne, ya dauki nauyin dokar dawo da tsohon taken Nijeriya, wanda ‘yan majalisar ke ganin harufan da aka yi amfani da su a cikin taken suna da ma’ana sosai kuma zai karfafa gwiwar al’ummar kasar nan wajen kaunar juna da hadin kai da kuma kyautata zamantakewa.
Sanata Rufa’i Hanga yana cikin masu wannan tunanin da ya ce tsohon taken Nijeriya waka ce da za ta kara karfafa kishin kasa a tsakanin ‘yan Nijeriya wadanda suka rayu cikin wannan zamanin, kuma sun fahimci muhimmiyar rawar da ta taka a tarihin al’ummarmu.
Hanga, ya ce taken Nijeriya da ake amfani da shi yanzu sojoji ne suka kawo shi kuma bai yi ma’ana kaman tsohon ba shi ya sa majalisa ta yi gaggawar amincewa da dokar saboda yaran wannan zamani su yi koyi da kalmomin taken domin ya sauya musu tunani.
Sai dai dan majalisar wakilai, Mohammed Shehu Fagge ya yi suka ne kan matakin da aka dauka na dawo da tsohon taken, inda ya yi tsokaci cewa, kawo wannan magana na sauya taken rashin sanin ciwon kai ne.
DUBA NAN: Sunusi Lamido Ya Bar Ribas Bayan Sanarwar Maida Shi Sarki
Shehu, ya ce a wannan hali da ‘yan kasa ke ciki na yunwa, fatara da rashi da sauran abubuwa makamantansu su ya fi dacewa a mayar da hankali a kai.