“Ƴan bindiga sun mamaye ɗaruruwan ƙauyuka a arewacin maso yammacin Nijeriya, inda suka maye gurbin gwamnati da masu sarautun gargajiya.
A wannan hali da ake ciki, ba za a daɗe ba za su soma ƙwace ikon dukkan ƙananan hukumomi,” in ji Audu Bulama Bukarti.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohin da lamarin ya faru sun sha alwashin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙara ƙaimi wurin tabbatar da tsaro a
Harin da wasu ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Gidan Bakuso na ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya, inda sace ɗalibai 15 na wata tsangaya ranar Asabar ya sake jefa yankin cikin zulumi gabanin soma azumin watan Ramadan.
Ƴan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da gwamnatin ta jihar Sokoto ta ƙaddamar da rundunar tsaro ta ƴan sa-kai a yunƙurinta na shawo kan rashin tsaro da ya addabi jihar.
Kuma hakan na faruwa ne kwana guda bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma’a a Anguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe wasu mutane sannan suka yi garkuwa da wasu.
Kazalika, a dai jihar ta Kaduna, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata wasu ƴan bindiga sun kai hari a makarantar firamare da sakandare da ke ƙauyen Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun, inda a can ma suka sace ɗalibai da malamansu kusan 300.
Kwana guda kafin harin na Kaduna, wasu ƴan bindiga sun sace fiye da mutum 200, galibinsu mata da ƙananan yara ƴan gudun hijira a Gamboru Ngala a jihar Borno yayin da suka je daji domin saro itacen girki.
DANYEN AIKI
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohin da lamarin ya faru sun sha alwashin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da ƙara ƙaimi wurin tabbatar da tsaro a yankin.
A saƙon da ya fitar ranar Juma’a, shugaban ƙasar ya ce ya bai wa jami’an tsaron ƙasar umarni su “gaggauta” kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a wata makaranta a Kaduna
“Na samu bayanai daga manyan jami’an tsaro game da hare-hare biyu da aka kai a Borno and Kaduna, kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa za a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa, “Na umarci jami’an tsaro da na leƙen asiri su gaggauta kuɓutar da waɗanda aka sace sannan su tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki.”
Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa iyalai da ƴan’uwan mutanen da aka yi garkuwa da su a jihohin biyu sannan ya ce nan ba da jimawa za a kuɓutar da dangin nasu.
Sai dai mazauna yankunan da lamarin ya faru da kuma masu sharhi sun yi gargaɗin cewa rashin tsaro na neman ya ci gwamnatin Nijeriya da yaƙi sannan suka buƙaci a ɗauki ƙarin matakai na zahiri.
Mai sharhi kan sha’anin tsaro, Audu Bulama Bukarti, ya ce muddin gwamnati ba ta tashi tsaye ba, rashin tsaro a arewacin Nijeriya zai fi ƙarfinta.
DUBA NAN: Gwamnatin Katsina Ta Sauke Farashin Kayan Masarufi Saboda Azumi
“Ƴan bindiga sun mamaye ɗaruruwan ƙauyuka a arewa maso yammacin Nijeriya, inda suka maye gurbin gwamnati da masu sarautun gargajiya. A wannan hali da ake ciki, ba za a daɗe ba za su soma ƙwace ikon dukkan ƙananan hukumomi… Dole gwamnatin tarayya ta ɗauki babban mataki kuma nan-take don magance wannan matsala,” in ji Bukarti a saƙon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.