Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan basaraken arewa a garin Wase, Mai martaba Dauda Mohammed Suleiman sun sace shi.
Majiyoyi daga gari ciki har da shugaban jam’iyyar ADC na Wase, Honarabul Abdullahi Gadole sun tabbatar wa manema sace basaraken a yankin arewa Kawo yanzu rundunar yan sanda na Plateau ba ta ce komai ba game da lamarin kuma wadanda suka sace shi ba su tuntubi iyalansa ba.
Jihar Plateau – Yan bindiga a kan babura sun sake basarake a karamar hukumar Wase ta Jihar Plateau, The Punch ta rahoto.
Mazauna garin sun ce an sace basaraken, Mai Martaba Dauda Mohammed Suleiman na a lokacin da yan bindiga suka kai hari fadarsa a garin Pinau, daren ranar Litinin.
A Wata Fitacciyar Jihar Arewa.
Mazauni garin Wase kuma shugaban jam’iyyar Action Democratic Congress a karamar hukumar Wase, Hon. Abdullahi Gadole, ya tabbatarwa The Punch sace basaraken a Jos a ranar Talata.
Gadole ya ce tun bayan da yan bindigan suka sace basaraken zuwa wani wurin da ba a sani ba, mutanen gari sun bazama nemansa amma ba a dace ba.
Gadole ya ce: “Jiya (Litinin) ne aka sace shi.
Su (masu garkuwar) sun taho gidansa da ke garin Pinau a kan babura ne suka sace shi.
Tun lokacin, ba su mu ganshi ba kuma wadanda suka sace shi ba su tuntubi iyalansa ba. “Amma, mazauna gari suna cigaba da nemansa amma suna cikin rudani domin ba su san abin da za su yi ba kan lamarin.”
An tuntubi kakakin yan sandan Plateau, Alabo Alfred.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred, bai daga wayarsa ba da aka jira shi don jin ta bakinsa kan lamarin yayin hada wannan rahoton.
The Punch ta rahoto cewa dakarun sojoji da ke aikin tabbatar da zaman lafya a jihar a farkon watan Agusta, sun yi atisayen fatattakan bata gari a karamar hukumar Wase.
Yayin atisayen na kwanaki, an kashe yan bindiga guda takwasa da ke adabar garuruwa a karamar hukumar kamar yadda jami’in watsa labaran sojoji na Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa ya tabbatar.
Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa.
A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.
Source: LEGITHAUSA