APC za ta yi zaman gaggawa kan shugabanci a majalisar dokokin Najeriya.
A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne kwamitin gudanarwa na jam`iyyar APC zai yi wani zaman gaggawa kan rikicin neman shugabanci a majalisar dokoki ta goma da za a kafa.
A farkon makon nan ne jam’iyyar ta fitar da wata sanarwa da ke nuna ta kebe shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ga wasu shiyyoyin kasar.
A sanarwar, APC ta ware wa shiyyar Kudu Maso Kuduncin Najeriya kujerar Shugaban Majalisar Dattawa tare da ayyana sunan Sanata Godswill Akpabio a matsayin wanda zai rike wannan mukamin.
Sai kuma kujerar Kakakin Majalisar Wakilai wacce jam’iyyar ta bayyana sunan Tajudeen Abbas daga shiyyar Arewa maso Yammacin kasar.
Bisa ga dukkan alamu wannan matakin na jam’iyyar bai yi wa wasu ‘ya’yanta dadi ba lamarin da ya sa wasu daga cikinsu yunkurin bijire mata.
Wannan hali da ake ciki ne zai sa kwamitin gudanarwa na jam`iyyar ta APC ya gudanar da zaman gaggawar domin nemo bakin zaren warware matsalar.
Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano tuni wasu masu takarar kujerar Kakakin Majalisar Wakilai suka fara nuna goyon baya ga Mukhtar Aliyu Betara wani dan takara na daban wanda ba shi jam’iyar tasu ta zaba ba.
Su kuwa a bangarensu, ‘yan adawa na sauran jam’iyyu da ke majalisar sun ce kamata ya yi APC ta zauna da dukkan ‘ya’yanta da ke majalisar kafin ta dauki irin wannan mataki mai muhimmanci kan shugabanci.
Wani dan majalisa na jam’iyyar NNPP daga jihar Jigawa Yusuf Shitu Galambi ya ce dole ne su ma ‘yan adawa su yi magana domin shugabancin majalisar ba na ‘yan jamiyya daya ba ne.
“Za mu fitar da wanda muke ganin yayi mana mu zabe shi a matsayin shugabanmu” in ji Galambi.
Masana siyasa a Najeriya na ganin idan har ba a warware wannan rikicin ba to babu shakka za a iya maimaita abin da ya faru a zaben shugabannin majalisar a shekarar 2015.
Dakta Abubakar Kari Masanin siyasa ne a Jami’ar Abuja kuma ya ce komai na iya faruwa.
“Akwai alamun da ke nuna cewa wasu ‘yan adawa suna kitsa kunyatar da APC, zabin da ya rage wa zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu shi ne ya yi amfani da kwanakin da suka rage ya shawo kan ‘yan jam’iyyarsa dan su yi abin da jam’iyyar take so, ko kuma ya mika kai bori ya hau” a cewar Dakta Kari.
A shekara ta 2015 ma dai an samu irin wannan rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan jam’iyyar ta APC lamarin da ya sa jam’iyyar ta rasa shugabanci a majalisar dokokin kasar.