Yayin da ake tunkarar zaben 2023, jam’iyyar APC ta gano hanyar tarawa Bola Ahmad Tinubu kudin yin kamfen.
APC za ta kaddamar da wata manhaja da za ta ke karbar kudi daga ‘yan Najeriya domin ba Tinubu da Shettima tallafi.
Ba wannan ne karon farko da APC ke karbar kudi daga ‘yan Najeriya ba a lokutan kamfen, an yi hakan a 2015.
Majalisar kamfen din jam’iyyar APC mai mulki za ta kaddamar da wata manhajar tara kudin tallafi ga ‘yan takarar ta na shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a ranar Talata.
Kaddamar da wannan manhaja zai faru ne a cibiyar Civil Centre da ke kan titin Ozumba a yankin Victoria Island da ke birnin Legas da misalin karfe 11 na safe.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na daya daga cikin jiga-jigan da za su halarci wannan taro mai dimbin tarihi, rahoton Vanguard.
Majalisar kamfen din ta ce, wannan manhaja za ta ba ‘yan Najeriya daman tallafawa dan takararsu, wanda kuma sanananne ne a tarihin kafa tubakin ci gaban jihar Legas, haka nan Eagle Online ta tattaro.
Dalilin neman tallafi daga ‘yan Najeriya, inji jam’iyyar APC
A cewar majalisar: “Tallafin zai rage tasirin cike jakunkuna da kudi, zai ba ‘yan kasa jin ana tare dasu da kuma zurfafa dimokradiyya a kasar.”
Ba wannan ne karon farko da APC ta taba karbar kudi daga hannun ‘yan Najeriya da sunan yin kamfen ba, an yi hakan lokacin da Buhari ya tsaya kamfen a 2015.
A wani labarin kuma, kungiyar kare hakkin Musulmi ta ce akwai bukatar Musulmai ‘yan yankin su Tinubu su kada kuri’unsu ga jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
PDP ta fadi irin tanadin da ta yiwa ‘yan Najeriya idan Atiku ya ci zabe badi Kungiyar ta ce tun daga 1999 zuwa yanzu, Musulmi dan yankin Kudu maso Yamma bai taba rike kujerun shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.
MURIC ta ce wannan ne damar Musulmai daga yankin da su tabbatar da an kare muradansu ta hanyar zaban Musulmi dan yankinsu, wanda kuma shine Bola Tinubu.
Source:Legithausa