Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dage gudanar da zaben fidda gwanin da zai tsaya mata takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023, daga ranar 29 ga watan Mayu, zuwa 6 ga watan Yuni.
Sakataren watsa labaran jam’iyyar ta APC na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar sa’o’i bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta karawa jam’iyyu wa’adin lokutan da ta tsayar musu domin su gudanar da zaben fitar da gwani.
A jiya Juma’a ne dai hukumar INEC ta sanar da tsawaita wa’adin da ta baiwa jam’iyyun siyasar Najeriya na zabukan fidda gwani da adadin kwanaki shida.
Da farko dai wa’adin ranar 3 ga watan Yuni hukumar ta sanar, amma a yanzu ta maida shi zuwa tsakanin 4 da 9 ga watan na Yuni.
A wani labarin na daban mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yace biyayyar sa ga Najeriya ce kawai kamar yadda yayi rantsuwar kama aiki amma ba ga wani mahaluki ba kamar yadda wasu ke hasashe.
Yayin da yake jawabi wajen taron masu ruwa da tsaki a Jihar sa ta haihuwa, wato Jihar Ogun, wanda ya samu halartar Gwamna Dapo Abiodun da manyan Sarakunan Jihar, Osinbajo yace ba ya kai musu ziyarar yakin neman goyan baya bane, sai dai ya ziyarce su ne domin shaida musu aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin kasar.
Osinbajo yace rantsuwar aiki da yayi bayan nasarar zaben da suka yi, rantsuwa ce ga jama’ar Najeriya da yaran kasar da kuma makomar ta baki daya.
Mataimakin shugaban kasar yace ya tuntubi bangarori da dama dangane da aniyar sa ta tsayawa takara domin zama shugaban kasa, ciki harda shugaban Muhammadu Buhari kafin bayyana aniyar sa ga sauran ‘yan Najeriya.
Nayi kokari a shekaru 7 da na yi
Osinbajo yace a cikin shekaru 7 da yayi a matsayin mataimakin shugaban kasa ya bada gudumawa wajen aiwatar da sauye sauye a bangaren shari’a da kuma tabbatar da kare hakkokin alkalai.
Mataimakin shugaban kasar yace aiki da Buhari ya bashi damar fahimtar shugabanci a matakin koli da kuma sanya shi a matsayin wanda zai iya warware matsaloli masu girma kamar irin na tattalin arziki da tsaro da makamantan su.
Zan daura inda Buhari ya tsaya
Osinbajo yace yana da fahimtar aikin da zai iya dorawa daga inda wadanda suka gabace shi suka yi.
Goyon baya
Gwamna Abiodun ya bayyana cikakken goyan bayan sa ga takarar mataimakin shugaban kasar wajen zama shugaban kasa, inda yace yana da kwarewar da ake bukata wajen ci gaba da yiwa jama’ar Najeriya aiki.
Shima a nashi jawabi, Babban Basaraken Jihar, Alake of Egbaland, Oba Adeodotun Gbadebo ya tabbatar da kwarewar Osinbajo wajen tsayawa takarar, inda ya masa addu’ar sake dawowa fadar sa a matsayin shugaban Najeriya.