Jam’iyyar NNPP ta ribato Sanatan jihar Bauchi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Halliru Dauda Jika Sanata Halliru Dauda Jika ya fice daga APC bayan shan kashi a zaben zama ‘dan takarar Gwamna.
Arch. Audu Sule Katagum yana cikin jagororin da jam’iyyar ta rasa a jihar ana shirin zaben 2023.
Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa, Halliru Dauda Jika ya fice daga jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisa.
Solacebase ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022, Sanata Halliru Dauda Jika ya sauya-sheka ne zuwa jam’iyyar hamayya ta NNPP. 10 Sanatan ya shaidawa Duniya wannan mataki da ya dauka a wata wasika da ya aikawa shugaban APC na mazabar Kafin Madaki a garin Ganjuwa.
Halliru Dauda Jika ya godewa shugabannin APC da suka ba shi dama ya nemi takarar kujerar gwamna a zaben fitar da gwanin da aka yi kwanaki.
Takarar Gwamna a APC Jaridar The Gazette ta ce Sanata Jika ya shiga jam’iyyar NNPP ne bayan ya gagara zama ‘dan takarar gwamnan jihar Bauchi a APC a zabe mai zuwa.
Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) ya doke Sanata Jika a zaben tsaida ‘dan takarar gwamna. Abubakar ya samu kuri’a 370, Jika ya ci 278.
Jagororin NNPP tare da tsohon Gwamnan Bauchi Hoto: @SaifullahiHon Asali: Twitter Wata majiya ta ce magoya bayan Sanatan mai shekara 46 suka dage a kan cewa ya koma NNPP bayan ya rubuta takardar da ta tabbatar da barinsa Jam’iyyar.
Jika shi ne Sanata na biyu da ya shiga jam’iyyar ta NNPP daga APC a ‘yan majalisar Bauchi. Kafin nan, Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyyar hamayyar.
Sauran ‘yan APC na jihar Bauchi da suka sauya-sheka sun hada da Audu Sule Katagum wanda ya rike mataimakin gwamna a jihar a gwamnatin da ya wuce.
Sauya-shekar ta na nufin NNPP ta samu karin magoya baya a kananan hukumomin Ganjuwa, Katagum da sauran inda ‘yan siyasar ke da magoya-baya.
Lawan Yahaya Gumau ya bar APC Kwanaki kun ji labari Sanata Lawan Yahaya Gumau ya shiga jam’iyya mai kayan marmari. Gumau shi ne mai wakiltar kudancin jihar Bauchi a majalisa.
Bayan ya fice daga APC mai mulkin Najeriya da rinjaye a majalisar dattawa, Sanatan bai yi wata-wata ba, ya yanki fam a jam’iyyar NNPP domin ya sake takara. APC ta sake rasa Sanata da wasu Jiga-jigan ‘Yan siyasa zuwa NNPP a jihar Bauchi.