Babbar kotun tarayya dake zamanta a Uyo, ta yi watsi da zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar Akwa Ibom karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Alkalin kotun mai shari’a, Agatha Okeke, a hukuncin da ta yanke ranar Litinin ta soke sunan Akanimo Udofia, matsayin dan takaran gwamnan jihar na APC a zaben 2023.
Alkalin ta bada umurnin cewa a gudanar da sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14 masu zuwa, PremiumTimes ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan karar da Sanata Ita Enang, hadimin shugaba Buhari kan Neja Delta ya shigar.
Alkalin ta amince da jawabin cewa Akanimo Udofia wanda ya lashe zaben fidda gwanin ba dan jam’iyyar APC bane lokacin da akayi zaben.
Udofia, wanda ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sayi Fom din takara gwamnan na PDP amma ya gaggauta komawa APC bisa shawarar tsohon Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.
Alkalin tace Udofia bai cika sharrudan dokar zabe ba da ta bukaci mutum ya kasance dan jam’iyyar APC na akalla kwanaki 30 kafin ranar zaben fidda gwani.
Bayan soke zabensa, kotun ta ce kada a saka sunansa a sabon zaben fidda gwanin da za’a gudanar na APC.
Ita Enang a jawabinsa bayan hukuncin, yace: “Na godewa Allah bisa wannan hukunci.
Na godewa Kotu, na godewa dokar zabe, na godewa al’ummar jihar Akwa Ibom.”
Zaben shekarar 2023 dai yana ta karatowa a yayin da aka kada gangar zabe.
‘Yan takara suna ta yakin neman zabe a jihohi da kananan hukumomi da kuma matakin ‘yan takarar shugaban kasa.
SOURCE:LEGITHAUSA