Shugaban kwamitin sulhu na kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ta bukaci Saudiyya da ta daina goyon bayan gwamnatin Yemen mai murabus tare da gargadin sakamakon ci gaba da wannan nuna goyon baya.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Shugaban kwamitin sulhu na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Yusuff Al-Fishi ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “Akwai hanyoyi guda biyu a gaban kawancen masu wuce gona da iri: ko dai su janye hannuwansu daga kasar Yemen su yi watsi da sojojin haya da suke marawa baya, su bar su suyi rayuwa yadda suka zaba, ko kuma su ci gaba da tallafa musu da sadaukar da tattalin arziki, tsaro da zaman lafiyar Saudiyya.
Shugaban kwamitin sulhu na kasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi Saudiyya kamar yadda Jalal Al-Ravishan mataimakin shugaban gwamnatin ceto kasar Yemen ya yi gargadi ga Riyadh a matsayin martani ga gazawarta wajen warware matsalar jin kai a Yemen.