Ango Ya Yi Tsalle Ya Fada Kan Amarya Ta Fadi Kasa Warwas a Wurin Shagalin Aure.
Cece-Kuce ya barke a Soshiyal midiya kan wani Bidiyo da aka ga Ango da Amarya sun yi kasa rigis a wurin shagalin aurensu.
Angon na tsaka da ba da nishaɗi a wurin da aka keɓe domin rawa ba zato ba tsammani ya yi tsalle kan amarya.
A Bidiyon ban mamakin, bakin da suka halarci shagalin dake kusa da ma’auratan sun koma kallonsu yayin da suka faɗi ƙasa warwas.
Wani sabon Ango ya ja hankali a wurin liyafar bikinsa lokacin da rawa tai rawa har ya faɗa kan Amarya bisa tsautsayi.
A wani gajeren bidiyo da shafin @mufasatundedednut suka wallafa a Instagram ya nuna.
Angon na wata rawa mai ban dariya ba ƙaƙƙautawa a gaban Amarya wacce ta sanya fararen kaya.
Ba zato ba tsammanin, Sabon Ango wanda ke cikin farin ciki, ya yi tsalle ya faɗa kan Amarya ba tare da ya so hakan ba, abinda ya ba mutanen dake tare da su mamaki.
Abu ya zame wa mahalarta shagalin abin kallo yayin da sabbin ma’auratan suka faɗi ƙasa warwas lokaci ɗaya.
Babu bayanin abinda ya faru bayan haka ko dalilin Angon na aikata haka.
Ɗan takaitaccen bidiyon ya ja hankalin mutane da yawan gaske, waɗanda suka garazaya sashin Kwament suka tofa albarkacin bakunansu.
Kalli bidiyon abinda ya auku a nan Jama’a sun maida martani @rodney_platinummix ya ce: “Waɗan nan mutanen na gabashin Nahiyar Afirkan suna aure ne tamkar wasan kwaikwayo kuma abin takaicin aurensu ba ya ƙarko.”
@talktoyossy ya ce: “Ni kam na kasa gane salon faɗuwar Ango da Amarya a wurin rawar bikin aure.
Ni fa ina zarginsu.” @mokunfunope ta ce: “Idan aka mun irin haka a shagalin bikina to sai dai a tashi ko kuma a ci gaba da shagalin ba amarya.”
A wani labarin kuma Wani mutumi ɗan Najeriya ya koka kan hana shi jin daɗin matarsa tun lokacin da Allah ya albarkace su da samun ƙaruwa.
Mutumin ya bayyana cewa matar sa ta maida hankali kacokan kan ɗan da suka haifa kuma ya wallafa bidiyon abokiyar rayuwar tasa tare da yaron na kwance a gado.
Yayin da ya ga matar dagaske take, mutumin ya koma rokon ƙaramin ɗan ya tausaya masa ya koma wani gadon daban da aka siya masa.