Ana Bikin Zagayowar Ranar Rediyo Ta Duniya.
Hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta kebe wannan rana , musamman don tunawa da tasirin da kafar rediyo ke yi wajen kawo sauyi a rayuwar jama’a, da kuma irin rawar da take takawa wajen bayar da bayanan abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.
A Najeriya da Nijar Kamaru da Chadi, rediyo na ci gaba da zama na gaba gaba a matsayin kafa bi yawan bibiya, da ta fi bayar da bayanai ga jama’a.
Kwamaret Bishir Dauda, sakataren kungiyar Murar Talaka a Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa, a yammacin Afirka rediyo ita ce kafa wadda mafiyawancin al’umma ke saurare da samun ilimi da kuma samun nishadi.
Kwamaret Bishir Dauda, ya ce daga cikin tasirin rediyo shi ne kafin ka ga mutum daya yana karanta jarida, sai kaga mutum 100 suna sauraron rediyo saboda saukin ta’ammalin da take da shi.