An sake kai hari ofishin INEC a jihar Imo.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya ta tabbatar da kai hari kan ofishinta da ke ƙaramar hukumar Oru ta yamma a jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.
A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Lahadi.
Hukumar ta ce harin ya shafin babban ɗakin taro na ofishin tare da lalata kujeru da sauran kayyaki a ɗakin taron.
A ‘yan kwanakin nan dai ana samun yawaitar hare-hare kan ofisoshin hukumar a ƙananan hukumomin jihar.
A ranar Asabar ma dai rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta ce dakarunta sun samu nasarar daƙile wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne tare da wata ƙungiya mai ƙawance da ita da ake kira Eastern Security Network, da aka fi sani da ESN suka kai kan ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar Orlu da ke jihar.
Hukumar ta ce wannan shi ne hari na bakwai kan ofisoshinta a jihohi biyar cikin wata huɗu.
Read More :