An rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya
An rantsar da sabon shugaban Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma da girman tattalin arziƙi a nahiyar Afirka.
Bola Tinubu, mai shekara 71, shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan Fabarairun 2023, tare da alƙawarin haɓɓaka ƙasar – duk da cewa akwai jan aiki a gabansa.
Tinubu ya sha rantsuwar ne tare da mataimakinsa Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin ƙasar.
Sun karɓi mulki ne daga shugaba Muhammadu Buhari, yayin da ƙasar ke fama da tashin farashin kayan masarufi da ƙalubalen tattalin arziƙi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Yanzu haka ƴan takara na jam’iyyar adawa na ƙalubalantar zaɓen a kotu.
Sun bayyana cewa an yi maguɗi a zaɓen.
Sai dai shugaba mai barin gado, wanda ya kwashe shekara takwas yana mulki ya ce zaɓe ne mai cike da adalci.
Manyan baƙi daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da ma duniya ne suka halarci bikin rantsuwar.
Tinubu wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Legas, na alfahari da rawar da ya taka wajen farfaɗo da jihar, wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta ƙasar.
Magoya bayansa na cewa zai yi amfani da ƙwarewa da tunaninsa wajen mulkin ƙasar ta Najeriya mai yawan mutane sama da miliyan 200.
Sai dai ƴan adawa sun ce a yanzu ba shi da karsashin da zai yi irin aikin da ya yi wajen ciyar da jihar Legas gaba.
Tun bayan zaɓen shi a watan Fabarairu, Tinubu ya yi tafiya sau biyu zuwa ƙasashen ƙetare, wani abu da ya haifar da tababa game da lafiyarsa.
A 2021 ya kwashe watanni a biornin Landan wajen neman lafiya.