An nada Sheikh Nuru Khalid limamin wani masallaci a Abuja.
Malamin addinin Musuluncin nan da aka kora daga limancin masallacin unguwar Apo saboda ya soki gwamnatin Najeriya ya sami wani sabon aikin na limanci a Abuja.
Kwamitin wani sabon masallacin Juma’a a Abuja ya nada shi a matsayin sabon limamin masallacin.
Sanata Sa’idu Dansadau, wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin ‘yan majalisu da ke unguwar Apo ne ya kori Sheikh Nuru Khalid saboda bai yi nadamar kalaman da ya fada a hudubarsa ta ranar Juma’a ba.
A ranar ce Sheikh Nuru ya caccaki gwamnati kan yadda ta bari wasu ‘yan bindiga suka kai wani mummunan hari kan wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a arewacin Najeriya.
Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, limamin ya sanar cewa, “Ina son sanar muku cewa mun sami wani sabon masallaci, kuma daga ranar Juma’a mai zuwa za mu bude shi. Ga wadanda ke ganin an hana mu wurin yin wa’azi, to su sani cewa mun sami wata sabuwar cibiya.”
READ MORE : ‘Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya 11 a wani sansaninsu a Kaduna.
Sheikh Khalid ya kara da cewa: “Ko a jiya wani malami addinin Kirista ya kira ni kuma ya sanar da ni cewa ya saka bidiyon hudubar da nayi ta ranar Juma’a ga mambobin cocinsa domin su saurari abin da na ce. Hudubata a masallaci ta fusata wasu mutane, amma wasu mutanen sun yaba min a cocinsu kan hudubar.”
Ya kuma ce maimakon ya ji haushin wadanda suka kore shi kan hudubar, yana tausaya musu ne.