An Kashe Sojojin Mali 8, Wasu Biyar Kuma Sun Bata Bayan Da Faransa Sanar Da Janye Dakarunta.
Rundunar sojin Mali ta ce an kashe sojojinta takwas sannan biyar sun ɓata bayan wani hari da ‘yan tawaye suka kai a arewa maso gabashin kasar. Wannan yana zuwa ne kwanaki biyu bayan da kasar Faransa da ƙawayenta suka sanar da aniyarsu ta janye dakarunsu daga Mali,
inda suka kwashe kusan shekara goma suna yaki da masu Ikirarin jihadi.
Wata Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, sojojin sama na kasar Mali sun kashe mayakan kungiyoyin na yan ta’adda kusan 60.
Ana ci gaba da nuna fargaba a yankunan kasar da ma ketare kan batun tsaro sakamakon korar dakarun Faransa da kuma yadda sojojin hayar Rasha suka samu gindin zama a kasar.
A wannan makon kawai, mazauna kasar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe farar hula 40 a yankin Archam wanda yan kungiyar IS da sauran kungiyoyi masu ikirarin jihadi ke kai hare-hare