Wani rahoto game da matsalar tsaro a Nigeria ya ce an kashe sama da mutane 400 a watan Nuwamba kaɗai sannan satar jama’a ta ƙaru yawanci a arewacin kasar.
Rahoton ya kuma ce an yi kisan ne a jihohi 28 na Najeriyar a ƙananan hukumomi 115 a cikin watan Nuwamba kaɗai.
Kamfanin Beacon Consulting duk wata yakan fitar da rahoto kan binciken da ya yi game da matsalar tsaro a Najeriyar tare da bayar da shawarwari ga mahukunta.
A cewar rahoton, satar mutane a Najeriya ta ƙaru da kusan kashi 38 cikin dari a Nuwamba idan aka kwatanta da alƙalumman rahoton na watan Oktoba.
Alƙalumman sun nuna mutum 363 aka sace a sassan Najeriya a watan Nuwamba.
Rahoton ya kuma ce an samu raguwar yawan mutanen da aka kashe da kimanin kashi 41 a ƙasar idan aka kwatanta da rahoton watan Oktoba da kamfanin ya ce an kashe mutum 636.
Rahoton watan Oktoba ya nuna wata huɗu a jere ana kashe sama da mutum 600 a Najeriya tun a Yuni, watan da aka fi kashe mutane a Najeriya a 2021 inda aka kashe mutum 1031.
Rahoton ya nuna yadda kamfanin ya gudanar da nazari da bincike da tattara alkalumansu a watan Nuwamba. Da kuma girman barazanar kai hare-hare a arewacin Najeriya duk da matakan da gwamnatin tarayya ke dauka da jihohi.
A cewar rahoton alƙaluman sun haɗa da yawan mutanen da aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya da ma waɗanda jami’an tsaro suka kashe a bakin aiki, da kuma su kansu jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a fagen daga.
Akwai kuma ƙaruwar laifuka a yankin kudu maso yammacin Najeriya da yanayin zaɓe a jihar Anambra da fasa gidan yari da aka yi a jihar Filato.
Rahoton ya nuna yadda aka dawo da hare-haren ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a hanyar Abuja – Kaduna. Akwai kuma ƙaruwar rikicin da ya shafi na siyasa.