An kashe mutum 422 a jihohin Najeriya uku cikin wata ɗaya – Rahoto.
Wani rahoto kan sha’anin tsaro a Nijeriya ya ce a cikin jihohi guda uku na arewacin ƙasar kawai, wato Borno da Zamfara da Kaduna, an kashe mutum 422 cikin watan Oktoban 2022, sanadiyyar matsalar tsaro.
Rahoton ya ce waɗannan kashe-kashe sun faru ne sanadiyyyar hare-hare na ƴan Boko Haram, da kuma na ƴan fashin daji masu kai farmaki a ƙauyuka suna sacewa da kashe mutane.
Haka nan kuma an samu rahotanni na ƴan fashi masu tare hanyoyi, sai kuma artabu tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba masu adawa da juna.
Jihar Borno ce lamarin ya fi muni, inda aka kashe mutum 214 a cikin watan na Oktoba, sai Zamfara, inda aka kashe mutum 131, yayin da aka kashe mutum 77 a jihar Kaduna.
A faɗin Najeriya kuwa rahoton ya ce an kai hare-hare sau 484 a ƙananan hukumomi 237 na jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Sai dai duk haka rahoton ya ce an samu raguwar kashe-kashen a watan na Oktoba idan aka kwatanta da mutanen da aka kashe a watan Satumba, inda aka kashe mutum 861.
Rahoton ya ce babu rasa rai a jihohin Ekiti da Jigawa
Rahoton ya ƙara da cewa a cikin matsalolin tsaro da ake fuskanta, Najeriya ta ci gaba da fuskantar satar ɗanyen man fetur duk da ƙarin ƙaimin da jami’an tsaro suke ƙarawa wajen yaƙi da lamarin.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Consulting wanda ya fitar da rahoton ya ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce giɓin da ake da shi na rashin jami’an tsaro a yankin karkara.
Ya ƙara da cewa hakan na faruwa ne saboda rashin isassun jami’an tsaro a ƙasar ta Najeriya.
Rahoton na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce kafin a iya kassara irin waɗannan mahara da ke ƙalubalantar ikon gwamnati, sai hukumomi sun ci gaba da ayyukan fatattakar ‘yan bindigan kamar yadda suka faro a ƙasar.