An Kashe Mutane Da Dama A Wani Hari A Gabashin Kasar Congo.
Kamfanin dillancin labarun ( AP) ya ambato cewa; A wani hari da ake tsammanin kungiyar ‘yan tawaye ta; “ Allied Democratic Forces” ne su ka kai a garin Beni da ke gabashin kasar Congo, sun kashe mutane fiye da 10.
Kakakin soja kaftin Anthony Mwalushayi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarun AP labarin kai harin wanda ya faru a jiya Litinin.
Kakakin sojan kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya ci gaba da cewa; A halin yanzu muna ci gaba da gudanar da bincike, kuma muna bin sawun abokan gba har zuwa kan iyaka da kasar Uganda.
READ MORE : Iran A shirye Take Ta Tallafawa Kasar Qatar Wajen Karbar Bakunci Gasar Cin Kofin Duniya.
A watan Maris da ya wuce ma an kai wani harin a gabashin kasar, wanda ya ci rayukan mutane 30. A watan Febrairu ma kungiyar ta ‘ya tawaye ta ; “ Allied Democratic Forces” ta kai da ya ci rayukan mutane 20.