An kashe farar hula 18 a Jamhuriyyar Nijar.
Farar hula 18 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hari da ƴan bindiga suka kai yammacin Jamhuriyyar Nijar, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta tabbatar.
Gwamnatin ta bayyana cewa ɓarayi riƙe da bindiga kan babura ne suka kai hari kan wata babbar mota da ke ɗauke da jama’a tsakanin wasu ƙauyuka biyu da ke yankin Tillaberi.
Yammacin Nijar- kamar Mali mai makwaftaka da Burkina Faso sun shafe shekaru suna fuskantar hare-hare daga mayaƙa duk da ƙoƙarin da dakarun ƙasashen waje ke yi waɗanda aka jibge a yankin Sahel domin yaƙar masu iƙirarin jihadi.
A yanzu wasu daga cikin ƙasashen da ke makwaftaka da Nijar ɗin na ƙarƙashin mulkin soji bayan shugabannin sojojin ƙasar sun hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.