An kama mai gidan abinci bayan kwastomominsa sun kamu da ciwon ciki
An kama mamallakin wani ɗakin cin abinci, da babban mai dafa abincinsa a jihar Kerala ta ƙasar India bayan mutuwar wata mata wadda ta rasu bayan cin abincin da ta saya daga ɗakin.
Wadda ta mutun wata ma’aikaciyar jinya ce wadda ta sayi abincin ta intanet.
Ƴan sanda sun ce akwai wasu mutanen 21 waɗanda suka kamu da rashin lafiya bayan cin abinci daga ɗakin na sayar da abinci.
A yanzu ƴan sandan sun gurfanar da mamallakin wurin sayar da abincin da babban mai dafa abincin da laifin kisan kai da gangan.
Lamarin dai na cikin jerin irin sa da aka samu a jihar, inda aka fara nuna damuwa game da tsaftar gidajen sayar da abinci.
An kwantar da Rashmi Raj, wadda ma’aikaciyar jinya ce a kwalejin karatun harkar lafiya ta Kottayam, a asibiti ne ranar 30 ga watan Disamba, lokacin da ta fara rashin lafiya bayan cin shinkafa da gasassar kazar da ta sayo daga ɗakin abincin.
Allah Ya amshi ranta ne a ranar biyu ga watan Janairu.
Bayanai daga kafafen yaɗa labaru a yankin sun ce binciken da aka yi ya gano cewar ta mutu ne sanadiyyar cutar da ta shafi ƴan hanjinta.
An kuma samu mutane da dama waɗanda suka kamu da rashin lafiya sanadiyyar cin abincin da suka saya daga ɗakin.
Ƴan sanda sun ce bincikensu ya tabbatar cewa ciwon cikin da abincin ya haddasa mata ne sanadiyyar mutuwar tata, kuma tsaftar abincin da ake sayarwa a ɗakin tana da rauni.
Ko a makon da ya gabata an samu rahotannin waɗanda suka kamu da ciwo sanadiyyar cin abinci.
A gundumar Pathanamthitta kuwa kusan ɗalibai da dama ne suka kamu da rashin lafiya sanadiyyar cin abinci a lokacin wani gangami.
Haka nan a yankin an samu wasu mutanen kusan 100 waɗanda suka yi rashin lafiya bayan cin abinci a wurin aikin ibada.
Tun daga wannan lokacin ne jami’ai masu kula da tsaftar abinci suka kai samame a ɗakunan sayar da abinci guda 500 a faɗin jihar.
An kuma dakatar da wauraren sayar da abinci guda 48 saboda rashin tsafta wurin gudanar da aiki da kuma rashin samun takardar izinin aiki.
Mahukunta sun ce za a ci gaba da kai wannan samame.
An kai irin wannan samame a watan Mayu na 2022, bayan da wani yaro ɗan shekara 16 ya mutu, wasu da dama suka yi rashin lafiya bayan cin abincin da aka haɗa a wata mashaya da ke lardin Kasargod.